Wani sabon salon cin zarafin mutane da tonan asiri da ya bullo a wannan zamani na ci gaban kimiyya da dama da ake dashi na saka komai a yanar gizo ya sa ba a daraja mutane da sirrin su kwata-kwata.
A ‘yan kwanakin nan wasu da basu da tarbiyya da sanin darajar sirrin mutane sun rika fidda wasu faifai na bidiyo da basu da kan gado matuka sannan da ke tozarta daraja da sirrin mutane a idanun mutane.
Ba wai ina goyon bayan abinda wadannan mutane suka yi ba ne amma sirrin su ne ake tonawa sannan a baza wa duniya su gani.
Idan kai da ka watsa wannan faifai aka bincike ka kila ba za ka tsira da mutunci ko da ta anini ce.
Sannan kuma mene ne dalilin daukar irin wannan bidiyo tun a karon farko. Sam ba shi da amfani domin kai da ka dauka ko kuma ke da kika dauka tare da kai/ke ne aka aikata wannan abu da ka/ki ka yada wa idanun duniya.
Ko a musulunci ya tsawatar da yin haka wato mutum ya tona asirin wani ko wata. Yin haka saba wa umarnin Allah ne, ballantana har ya kai ga na tsiraici ne.
Mutane su rika yi wa kan su adalci su daina yada irin wannan bidiyo na mutane ko kuma su rika dauka ma tun a farko.
Na farko dai ka tozarta wanda ka bayyana bidiyon sa a idanun mutanen da yake jin kunya, sannan yana da ‘ya’ya, Yan Uwa da iyaye da dai sauransu.
Ba zai sake yin tasiri a idanun wasu ba sannan ka cutar da shi kenan har a tunanin sa da rayuwar sa a dalilin abin da bai zama maka dole ka yi ba sannan kuma abinda ya shafi tsiraicin mace.
Ire-iren wadannan abubuwa dake ta yaduwa musamman yanzu ga ‘yan Arewa ya zama abin tashin hankali matuka.
Idan ma da gangar ne masu saki da yada irin wadannan faifai suke yi su yi wa Allah su ji tsoron Allah su dai na. Na wasu aka sani ba a san nasu ba. Idan Allah ya ce zai tona na su kila sai an kwantar da su a asibiti.
Allah ya kyauta.