Gwamnatin Tarayya na kan wani kwakkwaran shirin inganta tsaro a fadin kasar nan, ciki kuwa har da batun gaggauta daukar sabbin sojoji domin a kara yawan jami’an tsoron da za su shawo kan lamarin.
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin Shugabannin Kungiyar Fastocin Zaman Lafiya na Arewa.
Osinbajo ya shaida musu cewa Gwamnatin Tarayya na yin dukkan abubuwan da suka dace ta yi, wajen ganin cewa ta inganta tsaro sosai a kasar nan baki daya.
Ya ci gaba da nuna irin kokarin da gwamnati ke yi wajen inganta tsaro, ya na mai cewa.
“Gwamnati na bakin kokarin ta kwarai wajen inganta tsaro. Shi ya sa za mu gaggauta saukar sabbin sojoji, a cikin gaggawar da ba a taba yin saurin daukar sojoji kamar wannan lokacin ba.
“Ko a taron Majalisar Zartaswa da muka yi a ranar Alhamis, an zartas da batutuwa da dama game da tsaro, ciki har da karin daukar sojoji a cikin gaggawa, sayen makamai da kuma inganta tsaro ta sauran fannoni kamar jami’an tsaro na CJTF.”
Osinbajo ya ce yayin da ake ta wannan kokarin, akwai kuma gagarimin shirin dakile hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa ke yi a Arewaci da Kudancin kasar nan.
Buhari ya jinjina wa Kungiyar Kiristocin, kuma ya yi kiran a ci gaba da zaman lumana a tafiyar zamantakewar al’umma daya a kasar nan.
Bishop Mbayo Jpanet tun da farko ya bayyana wa Osinbajo cewa sun kawo ziyarar ce domin nuna goyon bayan su ga gwamnati.
Ya kuma bayyana Osinbajo a matsayin adalin limamin zaman lafiya.