Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa manyan masu ilmin kasar nan sun kassara Najeriya, ta hanyar kasa shawo kan matsalar tsaro a kasar nan, yadda ba a jin komai a kullum sai zubar da jinainan dimbin mutane kawai.
Sultan na Sokoto wanda shi ne Shugaban Majalisar Harkokin Musulunci ta Najeriya, ya yi wannan bayani ne a rana ta biyu ta “Taron Ranar Gafarta Wa Juna”, wanda Jihar Filato ta shirya domin tunawa da wadanda rikice-rikicen kabilanci ko na addini ya halaka, tare kuma da gafarta wa juna.
An shirya taron ne a Dandalin Gafartawa a ke Jos, inda Sultan ya yi nasa jawabi, narar Juma’a, kuma rana ta biyu da fara taron.
Kungiyar Sake Wanzar Da Zaman Lafiya ta Filato ce da hadin guiwar Kungiyar Sasanta Sabanin Mabiya Addinai ta Kaduna ce suka fito da wannan yunkuri tun a cikin 2019.
Gwamnatin Jihar Filato ta yi na’am da wannan shiri har ta bayyana ranar 7 Ga Fabrairu cewa babu aiki, ta zama ranar Yafe Wa Juna.
Sultan Sa’ad ya yi kakkausan bayani a wurin taro inda ya nuna kararar laifin shugabanni wajen kasa warware matsalar rashin tsaro a Arewa.
“Shugabannin mu sun ba su yi mana jagoranci na kwarai ba, ta yadda za su kawar mana gagarimar matsalar tsaro a kasar nan. Wannan matsala abin tayar da hankali ce a kasar nan.
“Sai dai a halin yanzu hankalin ya fi tashi, kuma mun fi damuwa da matsalar da ta fi shafar mu a nan Arewa.
Daga nan ya roki jama’a a daure a yafe wa juna, tare da kara jan hankali a rungumi turbar zaman lafiya baki daya.
” idan har mutum zai yi wa Allah laifi, ya tsuguna ya na rokon afuwa, dan Adam shi wane ya da ba zai yafe wa wanda ya yi masa laifi ba?
Daga nan ya yaba wa Gwamna Solomon Lalong na Jihar Filato, saboda kokarin da ya yi na ganin an sake gina tubulan ginin dorewar zaman lafiya a Jihar Filaro.
Filato ta shafe shekaru 20 ta na fama da kashe-kashen kabilanci da na addini, tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya cikin 1999.