Daga yanzu dukkan mahukuntan kasar nan da manyan masu hali za su kaurace wa titin Abuja zuwa Kaduna.
Hakan ya faru ne ganin yadda wani kamfanin sufurin jiragen sama mai suna Misha Travels a yau ya kaddamar da fara jigilar fasinjoji a kullum daga Kaduna zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Kaduna.
Misha Travels ya fara wannan zirga-zirga a ranar Litinin din nan, wanda kuma shi ne kamfanin sufuri na farko da ya fara wannan jigila zuwa Kaduna kai-tsaye.
A mota dai tafiya ce ta sa’o’i biyu, amma tuni aka kaurace wa hanyar saboda garkuwa da mutane da ake yi ba kakkautawa a tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Yawancin jama’a duk sun koma su na shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, ko kuma daga Kaduna zuwa Abuja.
Daya daga cikin jami’an kamfanin sufurin jirgin saman mai suna Tope Popoola, ya ce bai kamata a ce ana jigila zuwa Kaduna daga Abuja ba, saboda kusanci.
Amma ya ce matsalar rashin tsaro ce ta sa aka fara wannan harkokin sufurin zuwa Kaduna ko kuma zuwa Abuja daga Kaduna.
Jirgin dai samfurin Bombardier CRJ ne mai cin fasinjoji 50 kadai.
Cikin shekaru hudu zuwa yau dai an yi garkuwa da daruruwan mutane tsakanin Abuja da Kaduna.
Ita kan ta hanyar jirgin kasa da jama’a suka koma su na bi, ta fara gamuwa da matsala, domin ko a ranar 25 Ga Janairu, sai da aka yi wa wasu fasinjojin jirgin kasa garkuwa da su a Rigasa, kusa da tashar jirgi.
Wani masanin harkokin sufurin jirage mai suna Yakubu Datti, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kamfanin Misha Travels sun yi tunani, ganin yadda matsalar tsaro ta yi kamari sosai a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
An Bar Talaka Cikin ‘Wahala da Fargaba’
Kirarin wannan kamfanin zirga-zirga dai shi ne: “No fatique, no fear’, abin da a Hausance ake nufin ‘Babu ruwan ka da wahala, ba fargaba’.
To a bisa dukkan alamu dai an bar talaka a cikin fargaba da gajiya, domin ba shi da kudinn shiga jirgin sama, sai dai ya hakura ya bi titi, cikin gajiyar rashin kyan hanya da kuma fargabar masu garkuwa da mutane.