Majalisar Tarayya ta bayyana cewa akwai yiwuwar Boko Haram na kara kaimin ta’addancin su ne daga tallafin da wasu manyan kasashen duniya ke yi masu.
Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Sojojin Kasa, na Sama, na Ruwa da Hukumar Leken Asisi ta NI, Honorabul Babajimi Benson ya bayyana haka a ganawar da ya yi da manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya, a ranar Laraba, a Majalisa.
An yi wannan taron ne da wannan kwamiti, mako daya kenan bayan da Majalisar Tarayya ta nemi manyan Hafsoshin Tsaron su yi murabus, saboda kara tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Sun yi wannan ganawa ce a ranar da zaratan rundunar ‘yan sanda suka bada sanarwar kashe kusan ‘yan ta’addar kungiyar Ansaru 250 a Kaduna.
Kuma a ranar ce aka harbo wani jirgin helikwafta na ‘yan sanda a wannan arangama da mahara a Kaduna.
Bayan kammala taro da kwamitin Majalisa kan Tsaro da kuma Manyan Hafsoshin Tsaro, Benson ya shaida wa manema labarai cewa, ya shaida wa haofaoshin tsaro cewa, “a bisa abin da muka tattauna, na shaida musu cewa akwai burbushin gaskiyar maganar da aka watsawa cewa Boko Haram na samun tallafi daga wasu manyan kasashen duniya.
“Wasu maganganun da muka tattauna ba abin da zan fito a waje ko a kafafen yada labarai ba ne ina yayatawa.
” Tun ana maganar Boko Haram, aka zo ana batun ISIS, yanzu kuma ana magana kan ISWAP.
Honorabul Benson ya ce duk sun fahimci bayanan da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya suka yi musu, kuma za su gabatar da batutuwan a gaban majqlisa, domin yaki da ta’addanci abu ne da ya shafi kowa da kowa.
Tun da farko dai kafin a umarci ‘yan jarida su fita a kulle kofa a fara ganawar sirri, sai da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gabajabiamila ya bayyana cewa, “mun gayyato Manyan Hafsoshin Tsaron kasar nan, domin yi mana bayanin yadaa a Najeriya ake ci gaba da kashe jama’a, tamkar babu jami’an tsaro.”
Da manema labarai su ka tambayi Benson cewa ganin yanzu sun dawo su na cewa manyan sojojin suna kokari sosai, ko za a iya cewa sun dawo daga ra’ayin su kenan na cewa manyan hafaoshin su yi murabus kawai?
Sai ya ce ai ko sun fada ko ma ba su fada ba, Shugaban Kasa wanda shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ne kadai ke da ikon cire su. Dama kuma shi ne da kan sa ya nada su.
Shi ma Gbajabiamila ya ce sai an tashi tsaye barun yadda za a kawo karshen kashe-kashe da sauran ayyukan ta”addanci a kasar nan.
Discussion about this post