Majalisar Malaman Kano ta ki amincewa da dokar hana barace-barace da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi sanarwa a ranar Talata a Kano
Shugaban Majalisar Malaman, Ibrahim Khalil ne ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke tattautanawa da ’yan jarida a Kano.
Ya ce hana barace-baracen da aka yi bai zo daidai da lokacin da ya dace a hana din ba, kuma ita kan ta gwamnatin jihar Kano din ta dauki batun da wani muhimmanci ba.
Khalil ya ce akwai matakai da ya kamata gwamnati ta dauka kafin ta hana barace-barace a kan titi.
“Ya kamata a fahimci Majalisar Malaman Kano, kuma a amince da maganar su cewa gwamnatin Kano ba da gaske ta ke yi ba. Kuma ba za ta iya hana barace-baracen ba.
“Kawai dai ta yi ne don ta dadada wa iyayen gidan su na kasashen waje, ko kuma don kawai su karbo kudi ko saboda a yi surutai na fatar baki kawai.
“Ko kuma dai kawai an zarge su da aikata wani aibi ne can daga wani, su kuma suka gaggauta shirya sanarwar haka barace-barace domin bagararwa kawai.” Inji Sheikh.
Khalil wanda ya yi suna sosai wajen kokarin ganin an hana barace-barace, ya bada takaitaccen tarihin yadda a baya gwamnatoci suka yi ta kokarin hana barace-barace, amma abin bai yiwuwa ba, saboda kawai ba a dauki matakain da ya kamata a dauka kafin a hana barace-baracen ba.
Ya ce kamata ya yi a fara tuntubar masu ruwa da tsaki, kuma a gano su wane ne mabarata na hakika.
“Hanyar da ya kamata a bi kafin a hana barace-barace ita ce a gano ainihin yawan malaman makarantun allo ko makarantun allon kan su. Saboda akwai almajiran karatun allo masu barace-barace.
“Sannan akwai kuma wadanda iyayen su ke turo su domin su shigo birni su yi bara. Akwai kuma musakai ko nakasassu masu yin barace-barace.
“To shirin ba zai yi nasara ba, har sai an ware ba’arin wadannan mabarata an shigo da tsarin da za a magance kowane bangare daga cikin su. Amma ita gwamnatin Kano ba ta yi hakan ba.
“Hana barace-barace ba zai yi tasiri ba har sai an samu goyon baya da hadin kan malaman allo. Sai an zauna da su, a ji dalilin da ya sa almajiran su ke barace-barace tukunna.
“Sannan a samo adadin yawan su. Idan ta gano wadannan, to za ka iya gano yawan mabaratan da ba almajiran makarantun allo ba.
Khalil ya ce ba za a iya hana barace-barace a Kano ba, ba tare da nema da kuma samun hadin jihohin da ke makwautaka da Kano ba.
Daga nan ya shawarci gwamnatin Kano ta tuntubi masu ruwa da tsaki da kuma wadanda hana barace-baracen zai shafa tukunna.