Majalisar Dattawa za ta saurari Kudirin kafa ‘Yan Sandan Jihohi

0

Ranar Talata ne Majalisar Dattawa za ta yi zaman sauraren Kudirin Neman Kafa ‘Yan Sandan Jihohi a kowace jiha.

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, dan PDP daga jihar Enugu ne zai gabatar da kudirin, wanda zai kunshi neman kafa ‘Yan Sandan Jihohi, Hukumar Kula Da ‘Yan Sandan Jihohi.

Za a kafa su ne bayan na tarayya da ake da su kuma daban.

Ba wannan ne karo na farko da za a gatabar da kudirin ba. Ekweremadu ya taba gabatar da shi a ranar 12 Ga Yuni, 2018, a zangon Majalisar Dattawan Bukola Saraki, amma bai samu karasawa zuwa Kwamitin Gyaran Dokokin Kasa ba. A lokacin kuma shi Ekweremadu din ne shugaban kwamitin.

PREMIUM TIMES ta yi ido biyu da kudirin, kuma ta tsakuro wasu daga cikin abin da ya kunsa, da suka hada da:

Kirkiro Hukumar ‘Yan Sandan Jihohi, wadda za ta kula da ‘yan sandan jihohi.

Kirkiro ‘Yan Sandan Jihohi a karkashin Hukumar ‘Yan Sandan Jihohi.

Gwamna ne zai rika nada Kwamishinan ‘Yan Sandan Jiha, bayan ya mika sunan sa a Majalisar Dokokin Jiha sun amince.

‘Yan Sandan Jihohi za su rika gudanar da ayyukan tsaro gwargwadon irin yadda Majalisar Dokokin Kowace Jiha ta Zartas da irin dokokin aikin da za su yi a jihar.

‘Yan Sandan Tarayya na nan a matsayin su, amma ayyukan su zai shafi ayyukan tarayya ne bai-daya. Ba za su shiga hurumin ayyukan da Majalisar Dokokin kowace jiha ta rattaba wa ‘yan sandan ta na.

Hukumar ‘Yan Sandan Jiha za ta rika tuntubar Hukumar ‘Yan Sandan Tarayya domin wasu shawarwari kan nadin mukamai da wasu muhimman batutuwa.

Hukumar ‘Yan Sandan Jiha za ta kasance wa’adin shekara biyar. Daga nan sai a rusa ta, a kafa wata.

Kudirin ya tanadi wa’adin Kwamishinonin ‘Yan Sandan Jiha.

Duk abin da Hukumar ‘Yan Sandan Jiha ta tanadar ko ta zartas a kan Kwamishinan ‘Yan Sanda, to kotu ba za ta soke ba.

Bayan an karanta kudirin a ranar Talata mai zuwa, daga nan kuma za a damka shi kai-tsaye ga Kwamitin Gyaran Dokoki na Majalisar Dattawa, domin yin nazari da gyare-gyare.

Sake bijiro da wannan kudirin ya biyo bayan yawaitar tashe-tashen hankula da ke faruwa a kasar nan, wadanda ake ganin sun fi karfin magancewar ‘yan sandan kasar nan, wadanda ba su wuce 300,000 ba.

Share.

game da Author