Kotun Sauraren Kararrakin Ma’aikata ta umarci Hukumar Sojan Najeriya ta gaggauta maida wani jami’in soja mai suna Mohammed Sulaiman a bakin aikin sa.
Wannan hukuncin ya fito ne daga hedikwatar kotun ta babban birnin tarayya, Abuja.
Kuma wannan ne karo na 6 da kotu ta bayar irin wannan umarni na maida kotu, tun bayan da aka kori wasu sojoji a cikin 2016.
Mai Shari’a Sanusi Kolo ya ce ritayar tilas da aka yi wa jami’an sojojin da dama cikin 2016, haramtacciya ce, kuma ya soke dakatarwar kuma daga yau Laraba ba ta da wani tasiri.
Ya ce har yau sojoji sun kasa gabatar da kwakkwaran dalilin da zai sa a kori Kanar Sulaiman daga aikin soja.
An dai yi wa Kanar Sulaiman da wasu jami’ai da dama ritayar dole, ba tare da ba su takardar gargadi ko tuhumar su da aikata wani laifi ba.
Mai Shari’a ya kuma umarci a biya Kanar Sulaiman dukkan albashi da sauran hakkokin kudaden sa da ba a ba shi ba, tsawon shekarun da ya kwashe ya na zaman-dirshan bayan an sallame shi.
Kafin kotu ta bayar da umarnin maida Sulaiman a aikin sa, ta bayar da wani umarnin maid’s wasu jami’an sojoji hudu bakin aikin su.
Manyan jami’an da aka maida aikin a shekarar da ta gabata sun hada da Manjo Janar Nwomojo Ijeoma, Kanar Danladi Hassan da wasu Laftanar Kanar guda biyu.