A ci gaba da tsakure cikin littafin da Farida Waziri ta buga na tarihin gwagwarmayar rayuwar ta, a yau kuma mun karkato kan labarin da ta bayar a kan tsohon babban jami’in soja Lawan Gwadabe, wanda ta ce shi ma an yi masa sharrin ya na da hannu a yunkurin juyin mulkin da gwamnatin Abacha ta ce an yi mata cikin 1995.
Ga tsakuren daga bakin Farida a cikin littafin ta.
“Lawan Gwadabe jajirtaccen soja ne, wanda ba shi da tsoro ko kadan. Kuma jarumi ne na gaske. Domin duk da irin tsananin azabar da aka shafe kwanaki ana gasa masa, bai karaya kk kadan ba, kuma bai yarda ya fadi sunan kowa ba.
“Su kuma masu bincike, saboda wani kullin da suka kulla, sai suka nuna lallai Gwadabe ya na da hannu a yunkurin juyjn mulkin, wanda kuma duk karya ce kawai. Sai suka rika azabtar da shi da nufin wai sai sun ji wani abu daga bakin sa.
“A gidan da mu ke zaman binciken wadanda ake zargi aka tsare Gwadabe. Amma lokaci zuwa lokaci masu bincike kan fitar da shi, su kai shi wani wuri can su na azabtar da shi.
” Akwai ma wata rana da suka fice da shi sa sassafe. Ba su maido shi ba, sai wata safiyar suka shigo da shi a galabaice, ya yi laga-laga, ko tafiya ma ba ya iya yi.
“An sha bada umarni daga sama cewa a yi masa azabar ‘shan lugude’. MO kuma a jigata shi kafin a fara yi masa tambayoyi.
‘Shan lugude’ wata kwaya ce ake ba wanda ake zargi ya sha, domin ya fadi wasu bayanai. To akwai ranar da kwayar nan ta janyo jangwam, domin ta sa Gwadabe ya suke, ya kasa maida numfashi, sai da kyar.
“Nan da nan fa masu binciken sa suka gigice, suka firgice.”
A cikin littafin mai shafuka 224, Farida ta ce masu yi wa Gawadabe bincike sun gigice ne, saboda ba a ce au kashe shi ba. Kuma sun ji tsoron kada ya mutu ba su tatsi bayanan da suke son tatsa a wurin sa ba.
“Da suka ga sun yi duk irin azabar da za su yi, amma Gwadabe bai yi ko gezau ba, sai wani ya ce, ‘an ce duk duniya babu abin da Gwadabe ke so irin matar sa Khairat. Don haka a kamo ta, a yi mata azaba. Watakila ya shaida mata wani abu, wanda ita din za ta iya faurtawa.”
“Ni kuma ina jin haka, sai na mike, na ce ban ga dalilin da zai sa a kamo mace don ta na matar wanda ake zargi, a ce wai a gasa ma ta azaba.
“Na ce kowa a nan ya san idan sojoji za su juyin mulki, ba shaida wa matan su halin da suke ciki za su yi ba.”
Da wannan dalilai da na bayar ne, saboda na ga za a gallaza wa mace azaba haka kawai, sai suka hakura daga kawo matar Lawan Gwadabe.”