Lakada wa ma’aikatan lafiya duka da ‘yan uwan marasa lafiya ke yi a asibitocin Abuja na neman ya wuce gona da iri – ARD

0

Shugaban kungiyar likitoci (ARD) Adejo Arome ya koka kan yadda ‘yan uwan marasa lafiya ke yawan lakadawa ma’aikatan lafiya dukan tsiya a asibitocin Abuja.

A wani takarda da aka raba wa manema labarai a Abuja, Arome ya yi barazanar daukar mataki inda har jami’an tsaro basu hukunta wadanda suka tozarta wani ma’aikacin kiwon lafiya da ‘yan uwan marasa lafiya suka yi wa wani a Abuja.

Ya ce wannan abin takaicin ya auku ne ranar Asabar a asibitin FMC dake Jabi a Abuja inda wani likita da masu gadin asibiti suka sha dukan tsiya a hannun mijin mara lafiya.

“A lokacin da wannan likita ke duba wata mata da bata da lafiya sai aka kira shi ya gaggauta zuwa domin duba jikin wani yaro da ke kwance a bangaren yara a asibitin. Kafin ya tafi sai ya gaya wa mijin mara lafiyar da yake dubawa.

“Da ya dawo sai ya iske wani likita daban na duba matar. Ko da ya nemi sanin dalilin haka sai mijin wannan mata ya rufeshi da duka.

“ Nan take aka kira masu gadin asibitin domin su kawo dauki ashe gogan naka ya kira wasu abokan sa guda uku inda suka zo suka yi wa likitan da masu gadin asibitin taron dangi.

Arome yace jami’an tsaro sun kama mutumin da abokansa uku amma aka sake su.

Idan ba a manta ba a watan Janairu 2020 kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa baza ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta kwato wa ma’aikatan kiwon lafiya hakkunan su ko da zai kai ga a shiga kotu ne.

Shugaban kungiyar rashen babban birnin tarayya Abuja Ekpe Phillips ya fadi haka a dalilin tozarta wata likita da wasu ‘yan uwan wani mara lafiya suka yi a asibitin Maitama.

Phillips ya ce ‘yan uwan wannan mara lafiyan sun lakadawa likitan duka sannan suka yi mata zindir a cikin mutane saboda likitan ta ki yin abin da suke so ta yi musu.

Share.

game da Author