Jami’an Kwastan sun damke sunki-sunkin makudan daloli har dala milyan 8,065,615 da aka kudundune a cikin ambulan daban-daban a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Kwanturola Janar na Kwastan, Hameed Ali ne ya bayyana haka ranar Talata a Lagos, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.
Ya ce an kama kayan ne a cikin wata mota, a lokacin da ake kokarin loda kudaden a cikin jirgi.
Sai dai kuma har yanzu bai bayyana sunayen wadanda aka kama din ba, kuma a ba fadi jirgin na ina ba ne, ko kuma inda zai je.
Amma Ali ya ce motar da aka kama dolin kudaden a cikin ta, ta Kamfanin Kula da Zirga-zirgar Jirage ce, wato NAHCO.
Wadanda ake zargin dai wani direban da ya tuko motar ne, sai kuma wani ma’aikacin kamfanin NAHCO duk an kama su, ana zargin su da laifin karkatar da kudade.
Ya ce an nannade kudaden a cikin ambulan-ambulan, wadanda kowace aka rubuta wa sunan wanda za a kai wa kudaden.
“ Daga ranar da aka kwace wadannan kudade, har yau din nan babu wani banki da ya zo ya yi ikirarin cewa kudaden na sa ne.” Inji Ali.
Farkon hawan Shugaba Muhammadu Buhari dai an fara murna ganin yadda aka fara kama makudan kudade daga hannun wadanda ake zargi da wawurar kudaden gwamnati.
Sai dai kuma da tafiya ta yi nisa, an rika dawowa daga rakiyar gwamnatin Buhari, bisa zargin yadda gwamnatin da jami’an hana wuru-wuru ke kauda kai daga bincike ko tuhumar wasu da ake ganin cewa makusantan gwamnati ne.
Yawan bashin da gwamnatin Buhari ke ciwowa ba kakkautawa da kuma dimbin harajin jiki-magayi da ake lafta wa jama’a, ya sa an rika tambayar neman sanin abin da ake yi da kudaden da ake kwatowa daga hannun wadanda aka ce an kwato kudaden daga hannun su.