Hukumar Hana Fasa Kwauri, a Kano da Jigawa sun yi shiri tsaf domin fara fasa kantina suna kwace shinkafar waje da sauran kayan masarufin da aka hana shigo da su.
A cikin wata wasika da suka aika wa dukkanin manyan katinan zamani, wato ‘supermarkets, mai lamba NCS/KAN/053/S.28 a ranar 17 Ga Fabrairu, 2020 sun ce za su kwace duk wasu kayyakin da aka haramta shigo da su.
Sai dai kuma wasikar ba ta bayyana ranar da za su fara shiga su na kwace kayan masarufin ba.
Hukumar ta ce wannan farmakin kamen kayan masarufi za a fara shi ne da nufin dakile fasakwaurin kayan da aka haramta shigo da su domin a inganta tattalin arzikin kasar nan.
“ Mu na ganin ya dace mu sanar da ku neman hadin kai daga gare ku, domin ku daina sayowa ko sayar da shinkafar waje da dukkan sauran kayan da gwamnati ta hana shigo da su.
“ Idan ku ka yi haka, to za ku kauce wa fushin Jami’an Kwastan da za su rufe kantinan ku.” Haka sanarwar ta bayyana.
Tun bayan sanarwar rufe kan iyakoki jami’an kwastan da sauran jami’an tsaro a kan iyakokin Jihar Jigawa ke fama da dauki ba dadi da masu fasa kwauri, wadanda ke bin wasu hanyoyin shigo da kayayyakin da gwamnati ta haramta shigo da su.
Alamomi da korafe-korafe na nuna cewa wannan gargadi an yi shi har a jihar Katsina, kasancewa PREMIUM TIMES HAUSA ta samu labari mai kama da wannan.
Sannan kuma ana kukan cewa jami’an kwastan sun hana sun kama buhunnan aya da dabino da aka shigo da su daga Jamhuriyar Nijar.
Discussion about this post