Wasu kungiyoyin kare hakki guda uku sun nuna rashin amincewa da hujuncin kisa wanda Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun FCT, Abuja ya yanke wa Maryam Sanda.
Halilu ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ne ta hanyar rataya, bayan da ya bayyana gamsuwa da shaidun da aka gabatar masa, wadanda ya ce sun nuna Maryam ta aikata kisan.
Sannan kuma wadannan kungiyoyi uku, sun bayyana cewa Mai Shari’a Halilu ya yi azarbabin yanke mata hukunci, kana kuma wajen yanke hukuncin, yi a tsanake ba, sai ya yi ‘birgi-birgi-sallar-kura’, ya ce a rataye ta.
Kungiyoyin uku sun hada da Kungiyar Bin Hakkin Hata ta ‘MAD’, ‘Make A Difference’, sai kuma ta Kare Hakkin Dan Adam wato HURIWA da kuma ‘SOCEGE’
Dalilan Su Na Kin Yarda Da Hukuncin Maryam Sanda
Jami’ar ‘MAD’, Lemny Ughegbe ya ce akwai gaggawa da azaebabi wajen yanke wa Maryam hukuncin ratayewa da Mai Shari’a Halilu ya yi.
“Na karanta dukkan shafuka 100 na bayanan hukuncin da aka yanke mata. Na lura Mai Shari’a ya yi azarbabin yin birgi-birgi sallar-kura a hukuncin da yanke. Domin bai tsaya karba ko sauraren uziri da hanzarin da Maryam ta gabatar ba.”
Don haka wannan hukunci ba abin amincewa ko sahalewa ba ne. Halilu gaggawar yanke hukunci ba tare da yin cikakken Mazarin wasu batutuwa da ke a gaban kotun sa ba.
Lemny ya rika yanko wasu hujjoji a cikin Kundin Dokar Najeriya, ya na kafa hujja da su.
Shi kuwa Emmanuel Onmoniko na HURIWA da Mary Anietina ta SOCEGA, sun ce Mai Shari’a ya yanke wa Maryam hukuncin rataya ba tare da samun kwakkwarar shaida ko da guda daya ba.
“Gaba dayan shaidun da Mai Shari’a Halilu ya yi amfani da su, duk an-ce-ya-ce ne, babu kwakkwarar shaida ko guda daya ne da aka bayyana karara a kotu.
“Babu wanda ya bayar da shaidar cewa a gaban sa Maryam ta caka wa Bilyaminu wuka. Babu wanda ya ce a gaban sa aka yi komai ko a gaban sa ya fadi ya mutu ko kuma kafin ya mutu ya ce masa Maryam ce ta kashe shi.
” Shi kan sa abokin mamacin, wato Ibrahim Bilyaminu da ya shaida wa kotu cewa sau uku ya na karbarsa a hannun Maryam idan su na hayaniya da Bilyaminu, babu inda ya shaida wa kotu cewa Maryam ta taba suka ko yankar Bilyaminu da wuka.
“Sannan kuma shi da ke kwace wuka a hannun ta, ai ba taba yankar sa ba. To ya ba ta taba yankar mai kwace wuka har sau uku ba, amma kuma za ta yqnki mijin ta da ta ke ciwon so da tsakanin kishi?
“Daga cikin masu bayar da shaida babu wanda ya ce wa alkali ya ga wukar da aka yi kisan da ita. Kuma ‘yan sanda shida da su ka bayar da shaida, duk bayaan su sun yi harshen-damo da na juna.”
Sun ce alkali ya yi amfani da hujjar an-ce-an-ce wato hearsay a hurumin da babu kwakkwarar hujja.
Wannan kuwa inji su, ba abin karba na ne a matsayin hujjar da za a yi amfani da ita wajen yanke hukuncin mai tsanani, irin hukuncin kisa.
Yanzu sai Maryam na da damar daukaka kara cikin kwanaki 90 daga ranar da aka yanke mata wancan hukunci.
Maryam ta shaida wa kotu cewa ba ta cake shi da wuka ba, amma su na cikin fada ne sauka fasa tukunyar Shisha, shi kuma Bilyaminu ya fada bisa fasasshiyar tukunyar Shisha, ta ji masa raunin da ya yi sanadiyyar mutuwar sa.