Ku Ji Tsoron Allah, Ku Daina Yada Labaran Karya Game Da Masarautun Mu Masu Albarka! Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkanin kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Ya ku al’ummah, babu shakka, kowa dai yasan da cewa karya haramun ce a Musulunci, kai da ma dukkanin sauran addinai. Don haka kenan wajibe ne a kaurace mata ta ko wane irin hali, matukar dai muna son rabauta duniya da lahira!

Murtadha Gusau

Murtadha Gusau

Masu kokarin wallafa labaran karya na rubutu, da na hotuna, da na bidiyo a soshiyal media su ji tsoron Allah. Domin su sani, duk abunda suka rubuta ko suka yada, Allah Subhanahu wa Ta’ala zai tambaye su akai. Abin haushi da ban takaici shine, mutane ba su tsayawa su tantance labari, kawai sai su rubuta a shafukan su, ko su yada shi, domin neman suna, ko neman mabiya ko dai don biyan wata bukata. Wasu kuma burin su shine ace sune suka fara ba da labarin, kuma akasarin labaran na karya ne. Alal misali, a jiya alhamis, 06/02/2020 muka wayi gari da wani labarin karya, na kanzon kurege, yana yawo a soshiyal media game da masarautar Kano Mai albarka. Makiya wannan masarauta mai daraja, sun bi duk hanyoyin da zasu bi domin ganin cewa sun zubar da mutuncin wannan masarauta, amma Allah bai yarda ba kuma bai basu sa’a ba. To yanzu shine suka mayar da hankali wurin yada labaran karya akan wannan masarauta don ganin sun cimma burin su, wanda da yardar Allah ba zasu ci nasara ba!

Sun yada wani labari cewa wai masarautar Kano ta yi umurni ayi wasu addu’o’i saboda matsalar rashin tsaron da ke addabar Najeriya da ma arewa baki daya. Eh, masarautar Kano karkashin jagorancin jagora nagari, adalin Sarki, Malam Muhammadu Sanusi II, zata iya sa ayi addu’o’i akan wata matsala da ta damu al’ummah, kuma kullun ma a cikin addu’a suke, to amma idan masarauta za ta yi wannan, ba haka take yi ba. Masarautar Kano mai daraja tana da hanyoyin da take bi wurin gudanar da al’amurran ta, ba irin wannan da aka yi mata karya aka yada da sunan ta ba! Don haka ya zama wajibi muyi hattara kuma muji tsoron Allah. Ga sakon karya nan da ake yadawa a soshiyal media, wai da sunan masarautar, na sa a wannan rubutu nawa, ba tare da na canza komai ba, domin mu karanta. Lallai mai karatu zai ga cewa wannan sako ba daga masarautar Kano ya fito ba. Domin ba haka masarautar ta ke aika sakon ta ba, bare ma ace muhimmin sakon da ya shafi kula da rayukan al’ummah da dukiyoyin su irin wannan. Don haka muna kira ga masu yada irin wannan labarin karya, da su ji tsoron Allah su daina, idan kuwa ba su daina ba, to su sani wallahi akwai ranar kin dillanci… Ga karyar da suke yadawa kamar haka:

“SAKO DAGA FADAR MAI MARTABA SARKIN KANO.Assalamu Alaikum ya ‘yan’uwa musulmai:- munaso duk wanda ya samu wannan sakon ya sanar da ‘yan uwa musulmai cewa atashi ayi nafila Raka’a biyu, Raka’a ta farko a karanta fatiha da tabbat’yada kafa uku, Raka’a ta biyu a karanta fatiha da kuma wamakaru makaran wallahu khairun makirin kafa bakwai da niyyan duk wanda yake da hannu a cikin wannan masifa ta kashe kashe da satar mutane da suka addabemu dafatan Allah (s.w.t) ya hallakasu gabadaya kamar yadda Allah ya hallaka fir’auna da jama’arsa.. Dan Allah jama’a duk wanda ya samu ko yakaranta wannan sako yayi kokarin sanarda yan’uwa Musulmai, sakamakonsa yana daga Allah madaukakin sarki. PLS SHARE.”

‘Yan uwa, wannan shine labarin da suke yadawa. Yanzu da zan yi tambaya cewa, wai shin don Allah, don Allah, don Allah meye ribarku idan kun yada irin wannan labarin karya a soshiyal media akan wani ko wasu jama’ah? Shin ko kun san iya adadin mutanen da za su karanta wannan labarin karyar na ku kuwa? Shin yaya Mutuncin ku zai kasance a wurin wanda ya ga labarin daga gare ku, kuma daga baya ya gano cewa ba na gaskiya ba ne? Saboda haka ya kamata mu hada karfi da karfe mu tsaftace soshiyal media daga irin wadannan miyagun mutane masu yada labarin karya, ta hanyar yaki da kalaman batanci da labaran karya.

Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author