Kotu a Kano ta yanke wa wata mata mai suna Rashida Sa’idu ‘yar shekara 31 hukuncin kisa ta hanyar rataya a dalilin kamata da laifin kashe mijinta Adamu Ali da ta yi.
Wannan abin tashin hankalin ya auku ne ranar 20 ga watan Fabrairun 2019 a kwatas din Dorayi da ke karamar hukumar Gwale.
Rashida ta tunkudo mijinta Ali daga bene wai don ta ji yana hira da wata a wayar salula da kuma take zargi butuwarsa ce.
Dama kuma shi Ali matan sa biyu ne, Rashida da wata.
Tun a lokacin da Rashida ta fahimci akwai alamun mijinta zai kara aure sai ta garzaya wurin uwargida ta gaya mata. Ita uwargidan sai ta shawarci Amaryan, wato Rashida ta hakura kawai ta barwa Allah komai.
Ita kuwa Aisha bata saurari shawarar uwargidan ba sai ta tunkari mijin su wato Ali da kokuwa a daidai yana waya a saman bene. Aiko ta farmasa inda kafin ya ankare ta tunkudo shi daga sama.
Ali ya fado ya karya wuya, nan take ya mutu.
Rashida dalibar Ali ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano.
Sun haifi ‘ya’ya biyu tare.
Yanzu dai Rashida na da damar daukaka kara a kotun daukaka kara nan da wata uku masu zuwa idan har bata amince da hukunci da alkalin kotun Ahmad Badamasi ya yanke ba.
Idan ba a manta ba a watan Janairu ne babban kotun dake Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta rataya bisa kamata da laifin kashe mijinta Bilyaminu.
A yanzu dai Maryam ta daukaka kara a kotun daukaka kara na Abuja inda take neman kotun ta soke hukuncin kisa ta hanyar rataya da alkalin babbar kotun Yusuf Halilu ya yanke mata.
Discussion about this post