Babban kotun dake jihar Kaduna ta daure wasu mazaje biyu da ta kama da laifin kashe abokinsu da Adda.
Kotu ta kama Isah Yusuf mai shekaru 35 da Aminu Shu’aibu mai shekaru 32 da laifin hada baki wajen aikata kisan kai.
Alkalin kotun Hannatu Balogun ta dage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Maris sannan za a tsare Yusuf da Shu’aibu a kurkukun jihar har sai an kammala shari’ar.
Lauyan da ta shigar da karan Aisha Abdulmalik ta ce Yusuf da Shu’aibu sun kashe abokin su mai suna Shehu Abbas a watan Nuwamban 2019 a Unguwar Rimi Kaduna.
Aisha ta ce a bisa bayanan rahotan da suka samu Abbas ya rasu ne a dalilin saran addan da abokansa biyu suka yi masa.
Sai duk da wadannan hujojji Yusuf da Shu’aibu sun musanta aikata haka.
yanzu kotu ta ce a ci gaba da rike su a kurkuku har sai an kammala bincike sannan an yanke hukunci.
Discussion about this post