Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a bai wa Sambo Dasuki fasfo din sa na iznin fita kasashen waje. Dasuki shi ne tsohon mashawarcin shuhaban kasa a Harkokin Tsaro, a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Mai Shari’a Husaini Baba-Yusuf ya bada wannan umarnin ne bayan lauyan Dasuki mai suna Ahmed Raji ya rubuta takardar neman a bai wa wanda ya ke karewa din fasfo din sa.
Raji ya gabatar wa kotu kwararan dalilan neman a bayar da fasfo din, inda ya rika jawo wasu ayoyi daga cikin Kundin Dokokin Najeriya na Sashe na1, na 2, na 491 da kuma na 492(3) na 2015.
Lauyan ya ce fasfo din Dasuki ya wuce wa’adi da adadin shekarun da za a yi amfani da shi. Don haka akwai bukatar gaggauta sabunta shi.
Alkali ya amince kasancewa shi ma mai gabatar da kara bai yi wata jayayya a kan bayar da fasfo din ko kada a bayar ba.
Daga nan sai Mai Shari’a ya umarci Magatakardar Kotu ya bada fasfo din domin a je a sabunta shi, saboda ya wuce wa’adin da gwamnati ta amince a yi amfani da shi.
Daga nan sai aka daga sauraren karar zuwa ranar 13 Ga Maris, 2020 domin ci gaba da tanka shari’a.
Tuhumar Dasuki
EFCC ta gurfanar da Dasuki kotu, inda ake tuhumar sa da yin babakere a kan kudaden sayen makamai.
A cikin kara mai lamba FCT/HC/CR/42/2015, ana tuhumar sa ne tare da tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa da dan sa Sagir da kuma kamfanin Bafarawa mai suna Dalhatu Investment Limited.
Ana tuhumar su da laifuka 25, wadanda suka shafi kwashe tsabar kudi har naira bilyan 19.4.
Akwai kuma wata shari’ar ta daban, wadda ake tuhumar Dasuki ya karkatar da naira bilyan 33.2, tare da hadin bakin babban manajan NNPC, Aminu Baba-Kusa da wani kamfani.