Kotu ta bada belin makiyayin da aka yanke wa hukuncin zaman gidan Kaso a Benuwai

0

A ranar Alhamis ne kotun majistare dake Makurdi ta daure wani makiyayi mai suna Aliyu Jedi dake da shekaru 20 da laifin kiwo shannun sa a cikin gari.

Jedi ya nemi sassauci daga wajen kotun bayan ya amsa laifin da ya aikata.

A dalilin haka alkalin kotun Isaac Ajim ya yanke wa Jedi hukuncin biyan belin Naira 500,000 saboda wannan shine karo na farko da ya karya dokar hana kiwon dabbobi a jihar.

Ajim yace za a tsare Jedi a kurkuku har sai ya samu halin biyan kudaden belin.

Dan sandan da ya shigar da karar Hyacinth Gbakor ya ce hukumar kula da dabbobi na jihar ta kama Jedi yana gararamba da shannun sa a kauyen Tse-tswem dake Makudi ranar 12 ga watan Fabrairu.

An samu bayanin cewa Jedi dan karamar hukumar Langtang ne a jihar Filato. Ya shigo yankin Benuwai ne domin kiwo kamar yadda aka san fulani da yi. Sai dai yanzu maimakon zaman gidan kaso zai biya belin naira 500,000.

Idan ba a manta ba a watan Disamba 2018 ne Gwamnatin Jihar Benuwai ta bada sanarwar cewa Hukumar Kula da Dabbobi ta Jihar ta kwace wani garken shanu da aka kama ana kiwon su a sarari kusa da Babbar Kwalejin Akawe Torkula da ke Makurdi, babban birnin jihar.

Share.

game da Author