KOTU: Mahaifi ya musanta zargin cusa wa ‘yarsa hannu a gaba

0

Kotun Ikeja dake jihar Legas ta tsayar da ranar 30 ga watan Afrilu 2020 ranar da za ta yanke wa Emmanuel Idoko hukunci bayan kama shi da laifin cusa yatsun sa a farjin ‘yar sa mai shekara 12.

Alkalin kotun Sybil Nwaka ya tsayar da wannan rana ne saboda wadanda suka shigar da kara sun kasa bada hujojjin da ya kamata su nuna cewa Idoko ya aikata haka.

A dalilin haka lauyan da ke kare Idoko ya roki kotu ta yi watsi da wannan kara da aka shigar tun a shekarar 2017 saboda rashin kwararan hujojji.

Kotun ta fara shari’ar wannan cakwakiya ce tun a shekaran 2017 inda wani lauya mai suna Jide Boye ya kai karar mahaifin yarinyar bayan ya samu labarin abin da ya aikata.

Boye ya ce tsakanin watannin Yuli da Nuwamba 2017 a gidan su dake Oworoshoki a jihar Legas Idoko ya cusa yatsun sa a gaban ‘yar sa domin wai ya tabbatar da ko ta taba kwana da wani namiji.

Sannan kuma ya ce mahaifin nata wato Idoko ya ci gaba da muzguna wa yarinyar, yana tilasta mata da sai ta kwana da shi.

Boye ya kara da cewa sun samu tabbacin wannan labari ne daga wajen likitan asibitin ‘Mirabel Center’ bayan ya gabatar da sakamakon gwajin da ya nuna an aikata haka a jikin yarinyar.

Sai dai kuma mahaifin nata Idoko ya musanta aikata haka yana mai cewa ‘yarsa karya kawai take masa.

“Tun da nake ban taba ganin tsiraicin ‘yata ba ballantana har ya kai ga na nemi in kwanta da ita.

Idoko yace mutane sun kawo masa kara sannan shima ya samu tabbacin cewa ‘yarsa na yawon banza tare da wasu yara marasa tarbiya da hakan yasa nake ganin sun tafka ashararancin su ne kawai.

“ Ko da na tambayi ‘yata game da wannan Magana sai ta nemi ta dambaceni, ni kuma a matsayina na mahaifin ta sai na lakada mata dukan tsiya, shine ya kai ga har wai aka zargeni da saka mata yasa a farji.

Idoko dai zai saurari hukuncin da kortu ta dauka a kansa ranar 30 ga watan Afrilu.

Share.

game da Author