Kotu a Abuja ta dakatar da INEC daga soke rajistan jam’iyyu

0

Babbar kotu a Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) soke rajistan wasu jam’iyyun siyasa a kasar nan.

Alkalin kotun Anwuli Chikere ta yanke wannan hukunci ranar Litini da safe bayan wasu cikin jam’iyyun da INEC ta soke rajistan su sun kai hukumar kara.

Chikere ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda INEC ta kasa gabatar da kwararan hujojjin da za su doke wanda jam’iyyu suka gabatar ba tare da ta tauye musu hakkunan su ba.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta rage yawan jam’iyyun siyasa dake Najeriya daga 92 zuwa 18.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ya sanar da haka yana mai cewa hukumar sa ta yi haka ne bisa damar da tsarin mulkin Najeriya ya ba ta na iya yiwa jam’iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam’iyyun da suka ga ya kamata a soke ko dan rashin tasiri ko kuma a wani dalili da doka ya bata dama.

Hukumar ta ce ta yi kyakkyawar dubi da nazarin tasirin da jam’iyyu suka yi da irin rawar da suka taka a zabukan da aka yi a akasar nana har da wadanda aka yi a abaya-bayannan wato sake zabe da kuma cike gurbi.

Share.

game da Author