Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su canja salon yaki da Boko Haram idan har suna so su kawo karshen wannan ta’addanci.
Shugaban kungiyar Ayuba Waba ya sanar da haka da yake wa mutane da gwamnatin jihar Barno ta’aziya da jajen kisan kiyashi da Boko Haram suka yi wa matafiya a Auno ranar Lahadi.
Waba yace wannan ba shi ne karo na farko ba da Boko Haram ke kai wa mutane hari a jihar, ya ce ci gaba da kyale irin haka na faruwa zai dawo da hannun agogo baya na game da kokarin kau da su a kasar nan.
“ Kamata ya yi gwamnati da jami’an tsaron Najeriya su kirkiro sabbin hanyoyi da za a tunkari yaki da Boko Haram. Yaya za a ace har Boko Haram su far wa matafiya da ke zaune wuri daya suna kashe su sannan suna kwashe na kwashewa har tsawon awoyi hudu hankalinsu kwance ba tare da da jami’an tsaro sun far musu ba.
Wabba ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su karaya amma su kara kai kaimi wajen yaki da Boko Haram daga kasar nan gaba daya.
Idan ba a manta ba a daren ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 ne Boko Haram suka kashe mutane matafiya 30,banka wa motoci 18 wuta, sannan suka yi garkuwa da wasu a kauyen Auno.
Matafiyan sun yada Zango ne a Auno, kilomita 24 kusa da shingen tsaron sojoji kafin shiga Maiduguri.
Sojoji kan datse hanyar shiga Maiduguri tun 6 na yamma zuwa washegari, 6 na safe, babu shiga kuma ba fita.
A dalilin haka ne gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.
Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a daren Lahadi.
Discussion about this post