A daidai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje garin Maiduguri, matasa suka fito gefen titunan garin Maiduguri suna yi masa eho da sowa don nuna rashin jin dadin su game da harin da Boko Haram suka kai wa matafiya da suka yada zango a garin Auno.
Matasa sun rika cewa “Bama So, Ba ma Yi” a dai dai Buhari na wucewa.
Idan ba a manta ba a daren ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 ne Boko Haram suka kashe mutane matafiya 30,banka wa motoci 18 wuta, sannan suka yi garkuwa da wasu a kauyen Auno.
Matafiyan sun yada Zango ne a Auno, kilomita 24 kusa da shingen tsaron sojoji kafin shiga Maiduguri.
Sojoji kan datse hanyar shiga Maiduguri tun 6 na yamma zuwa washegari, 6 na safe, babu shiga kuma ba fita.
A dalilin haka ne gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.
Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a daren Lahadi.
Gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona gidaje da motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.
Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a Lahadi da dare.