KISAN KIYASHI: Majalisar Tarayya ta nemi a binciki kisan matafiya a Auno

0

Majalisar Tarayya ta nemi a gaggauta kafa kwamitin da zai binciki yadda aka yi sakacin da har Boko Haram suka yi wa matafiya dirar-mikiya suka banka musu wuta da bindige 30 a cikin su.

Majalisa ta ce abin mamaki da takaici ne ganin yadda garin na Auno ba ya da nisa da inda jami’an tsaro suka kafa shingen hana motoci shiga Maiduguri.

Bayan wannan majilisa ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa dokar-ta-baci akan harkar tsaro a kasar nan.

Sannan kuma ta nemi kwamitin ya binciki yadda ake zargin cewa zuciyar wasu sojojin masu yaki da Boko Haram ta fara yin sanyi. Watau guyawun su sun yi sanyi daga nuna irin zakakurancin da a da ake ganin sun fi nunawa wajen yaki da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya dora laifin kisan mutane 30 da kona gidaje da motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.

Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a Lahadi da dare.

PREMIUM TIMES ta bayar da labarin yadda Boko Haram suka banka wa motocin matafiya wuta, suka arce da wasu matafiya, bayan sun kashe wasu da dama a Auno.

Matafiyan sun yada Zango ne a Auno, kilomita 24 kusa da shingen tsaron sojoji kafin shiga Maiduguri.

Sojoji kan datse hanyar shiga Maiduguri tun 6 na yamma zuwa washegari, 6 na safe, babu shiga kuma ba fita.

“A gaskiya an tura ni har an kai ni bango. Tunda na kai makura, bari na fito na fadi gaskiya.” Inji Zulum.

“Daga ranar da aka rantsar da ni zuwa yau, Boko Haram sun kai hari a ganin Auno kamar sau shida kenan. Kuma dalili kawai shi ne saboda sun samu kofar kawo harin ne saboda sojoji sun janye daga Auno.

” Mun yi kira kuma mun sha yin roko ga sojoji su dawo da sansani, su kafa sansani a Auno. Amma ba su karbi roko ko shawarar mu ba har yau.”

Wani Kwamandan Bataliya da ke tare da Gwamna Zulum a lokacin, a garin na Auno, ya yi kokarin kare sojojin, inda ya ce akwai sojoji a garin, amma gwamnan ya gwasale shi.

“Ka ma daina cewa akwai sojoji. Saboda babu! Duk kiraye-kirayen da muka rika yi a girke sojoji a nan Auno, ba a ji mu ba.

“Ni ba fada ko jayayya ko fito-na-fito za mu tsaya mu na yi a nan da kai ba. Amma maganar sojoji dai a nan babu. Mun sha yin kira a kafa sansani a nan Auno, saboda Boko Haram sun maida garin wurin da ya fi saukin kai hari, amma na a amshi kukan mu ba.” Cewar Zulum.

“Da an ce karfe 5 na yamma ta yi, sojoji sun datse kofar shiga, sai su bar wurin su ma su shiga Maiduguri, su kyale dandazon matafiya a kan hanya, su na jiran a bude hanya gobe da safe.

“Idan za ka umarci sojojin ka su dawo su kafa sansani a Auno, to ka yi. Idan kuma ba za ka yi ba, to kawai ka fada mana. Mu kuma sai mu san abin da za mu yj, a matsayin mu na gwamnati.

“Don girman Allah ka dubi yawan rayukan da aka rasa a wurin nan. Idan ka na tababa, to ka matsa ka kidaya gawarwaki da kan ka.”

Daga nan Zulum ya nuna takaicin yadda aka yi wannan mummunan hari, tare da cewa, “Jami’an DSS sun kawo rahoton gargadin yiwuwar kawo hari, kamar yadda suka taba bada rahoton na Jakana, amma ba a yi komai a kai ba.

”Ni dai a daina duk wata doguwar magana. Don Allah ku dawo da sojoji, a matso da shingen sojoji a nan Auno. Saboda daga nan zuwa Jami’ar Maiduguri fa kilomita 8 ne kacal. To idan har ba za a iya kare lafiyar jama’a a nan da kuma da Jami’a ba, ai mu da ke cikin Maiduguri ma mu na cikin tashin hankali kenan. Domin abin da ya ci Doma, ba zai kyale Awai ba.” Inji Gwamna Zulum.

Harin Auno: Laifin Matafiya Ne – Babban Kwamandan Yakin Boko Haram

Babban Kwamandan Yaki Da ‘Yan Boko Haram, Olusegun Adeniyi, ya ce matafiya ne da kan su suka haifar da wannan mummunan hari da Boko Haram suka kai musu a Auno, inda suke yada zango su kwana.

Bayan ya nuna jimami, alhini da takaicin kisan, Adeniyi ya ce masu motoci sun ki bin umarnin da sojoji suka yi cewa idan yamma ta yi su kaurace wa titin Damaturu zuwa Maiduguri.

Ya ce mun sha sanarwa cewa idan direba ya san ba zai iya kaiwa ko shiga Maiduguri kafin ko karfe 5 na yamma ba, to kada ma ya kuskura ya biyo titin.

Adeniyi ya ce su na kulle hanyar ce a haka motoci gilmawa da dare domin cikin daren ne sojoji ke sintirin yaki da farautar Boko Haram a yankin.

“Da rana sojoji na aikin tsaron titi da masu tafiya kan titin. Idan dare ya yi kuma ana kulle titin ne saboda sintirin farautar ‘yan ta’adda sojoji ke yi.

“Don haka bai kamata wanda ya san motar sa ba ta da gudun da zai iya shiga Maiduguri ba, ya yi gangancin baro ganin Benisheik ba. Saboda ya san ba zai shiga Maiduguri ba, ba za a bar shi ba, sai dai ya kwana a kan hanya.” Inji Adeniyi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dora laifin yawan farmakin da Boko Haram ke kai wa a Barno a kan shugabannin jihar.

Ya ce al’umma da shugabannin jama’a ba su bayar da hadin kai ga sojoji domin kawo karshen Boko Haram.

Ya ce: “Wadannan masu kawo hari, ‘yan Boko Haram ake kiran su ko ma ‘yan me za a kira su, ba za su iya shigowa cikin Maiduguri ba ko kewayen ta ba tare da sanin shugabannin al’ummar yankin ba.”

Buhari ya fadi haka a lokacin da ya ke na shi bayanin bayan da Gwamna Babagana Zulum da Shehun Barno sun yi masa bayanin halin da ake ciki dangane da maharan.

Buhari ya kai ziyara ce a Maiduguri, mako daya bayan mummunan harin da Boko Haram suka kai wa matafiya a garin Auno, inda suka kashe matafiya 30 tare da kone motocin su da wasu gidaje 18.

Sai dai Buhari bai karasa har Auno, inda aka yi wa matafiya mummunan kisan ba.

Majalisar Dattawa Ta Fusata

Ganin yadda bai gamsu da dalilan da sojoji suka bayar ba, sai Shugaban Masu Rinjaye Mohamme Monguno ya bayyana cewa da an dauki kwakkwaran mataki, to za a iya kauce wa afkuwar halin.

Ya ce barin matafiya su san inda dare ya yi musu, bayan sojoji sun datse hanya, wannan sakin nauyin da aka rataya musu ne na kare rayuka da dukiyoyin Jama’a.

Shi ma Ahmed Jaha daga jihar Barno, kuma wakilin APC, ya goyi bayan Munguno, inda ya cika da mamakin cewa daga cikin motocin da aka datse aka hana shiga Maiduguri a ranar, har da tanka mai dauke da main a sojoji, kuma motar ta rundunar sojojin ce.

“Na dade ina mamakin yadda sojoji za su hana motar su shiga, duk kuwa da cewa kayan su ta ke dauke.

‘A Rika Barin Motoci Na Shiga Maiduguri’

Majalisa ta cimma matsayar a kyale motoci na shiga Maiduguri bayan karfe 6 na yamma. Ta ce a daina barin motoci na kwanan daji, su kuma Boko Haram su rika kai musu hari su na kashe na kashewa sun a sace na sacewa.

A na sa karin bayani, Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu, ya kara yin kira da lallai a cire kwamandojin sojjoji, wadanda ya ce duk wata basira da dabaru na su sun kare.

Share.

game da Author