Wata mataimakiyar darektan ayyuka dake aiki a fadar shugaban kasa ta bakunci lahira a ranar litinin inda wasu da ba a san ko su waye ba suka bita har gida suka kashe ta.
Laetitia Daga wanda ‘yar asalin jihar Filato ne ta rasa ranta ne ranar litinin da dare.
Mataimakiyar darektan yada labarai na fadar shugaban kasa, Attah Esa ta bayyana cewa Daga ta yi aiki ranar litinin har zuwa karfe 8 na dare kafin ta tashi daga aiki. Amma kuma da misalin karfe 11 na daren wasu suka far mata a gidanta suka kashe.
Babban sakataren fadar shugaban Kasa, Jalal Arabi, ya bayyana cewa lallai fadar Aso rock ta yi rashi matuka. Ya kara da cewa ‘Yan sanda za su cafko wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Sannan kuma ya yi wa iyaye, ‘yan uwan da duka ma’aikatan fadar shugaban kasa ta’aziyyar rasuwar Daga.