Shugaba Muhammadu Buhari ya ce babban matakin yin nasara a kan Boko Haram shi ne a daina yi masu kallon barazana ce ga zamantakewar kasan ko yi musu kallon suna kaddamar da yakin addini ne a kan wani addini ko mabiyan addinin.
Buhari ya yi wannan bayanin a shafin Twitter biyo bayan yamutsa gashin baki da ake yi a kasar nan, bayan kashe Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), na Karamar Hukumar Michika, Jihar Adamawa.
Ya ce Boko Haram sun dauko hanyar raba kai da hada mabiya addinai biyu fada a kasar nan, abin da idan aka sake aka yarda da su, to alama ce mai nuna Boko Haram sun yi nasara kenan.
Daga nan sai ya yi kiran ‘yan Najeriya su hada kai a kakkabe ta’addanci wanda ya mamaye kasar nan shekaru goma kenan.
Shugaban ya ce ba kamar yadda ake watsa cewa Boko Haram na hari kan Kiristoci ba, ya ce kashi 10 bisa 100 na wadanda Boko Haram ke kashewa musulmi ne.
Ya kawo misalai kamar kama daliban Chibok da hare-hare a kan masallatai, da kisan gillar wasu mashahuran malamai biyu na kasar nan.
“Wasu masu kokarin ganin sun raba kan mu sun hakikice su na yada cewa Boko Haram Kiristoci suka sa a gaba. Wannan kuwa ba gaskiya ba ne.
“Don haka kada mu sake MU bayar da kofa Boko Haram su kawo rarrabuwa tsakanin mu. Mu kasance tsintsiya daya cikin hadin kai da yafiyar juna.
Buhari ya ce ‘yan Najeriya ba su da wata kasa kamar Najeriya. Don haka a daina kallon masu kokarin tilasta wasu sai sun bi wani addini a matsayin su na yi sa addini wani abin kwarai ne.
Discussion about this post