Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, sun yi magana dangane da kallon da ake yi cewa Shugaba Muhammadu Buhari na jan-kafa wajen kin gaggauta tsige Manyan Hafsoshin Sojojin Kasa, Ruwa da na Dama, saboda ci gaba da tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Jama’a da dama na ci gaba da kiraye kirayen a cire su, domin tsaro na kara tabarbarewa, musamman Boko Haram, hare-haren ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da jama’a.
A kan haka ne a ranar Litinin Lawan da Gbajabiamila suka gana da Shugaba Buhari a cikin Villa, a Abuja.
Bayan fitowa daga taron, manema labarai sun yi wa su biyun tambayoyin neman karin bayani, inda Lawan ya fara amsawa.
“Mun tattauna duk wasu batutuwa da suka kamata mu tattauna tare da Shugaba Buhari, musamman batun tsaro.”
Yayin da Sanata Lawan bai yi wani karin haske ba daga nan, sai shi kuma Gbajabiamila ya ci gaba.
“Mun yi magana kan komai da ya gabata, musamman tun bayan da batun neman a tsige shugabannin tsaron kasar nan ya fara tasowa a majalis.
“Wato lamarin ne ya masu biyu. Na farko dai shi ne akwai masu ganin cewa dama wa’adin su ya wuce, Shugaban Kasa ne ya kara musu wa’adi. Duk da haka kuma matsalar sai karuwa ta ke yi. Don haka a cire su kadai shi zai fi.
“Sannan a gefe daya kuma akwai masu tsinkayen cewa me ya sa za a ga laifin sojoji a kan tabarbarewar tsaro a cikin kasa, kamar kashe-kashe a yankuna, garkuwa da mutane da sauran su. Su na ganin cewa wannan duk aikin ‘yan sanda ne, ba na soja ba. Aikin soja kare kasa daga hana a shigo mata da mamaya daga wata kasa.
“Suke ganin cewa sai a duba a bangaren Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a gani. Shin ya na ayyukan sa kamar yadda suka kamata, ko kuwa ba ya samun nasara? Shin cire manyan hafsoshi ne zai kawo karshen kashe-kashen?
Gbajabiamila ya nuna nuna cewa Shugaba Buhari ya damu kwarai da halin da kasar nan ke ciki. A ma su bangare a Majalisa kuma su na bakin na su kokarin da suke yi, domin shawo kan lamarin.
Discussion about this post