Wani magidanci mai suna Ibrahim Lawal dake da shekaru 58 ya kai karar matar sa Saratu Musa kotun shari’a dake unguwar Rigasa, jihar Kaduna kan cewa Saratu ta kaurace masa har na tsawon kwanaki 48.
Lawal dake da zama a Maraban Jos a jihar Kaduna ya bayyana wa kotu cewa yana matukar iya kokarinsa wajen ganin ya ciyar da suturtar da matarsa Saratu amma duk da haka ta ki yarda ya kusanceta duk lokacin da bukatar haka ya taso.
“ Har wa’azi na yi wa Saratu don ta fahimci illar yin haka amma duk da haka da ga na lallabo sai ta kauce ta yi kememe tace sam ba za a yi ba.
Ya ce a dalilin haka yake rokon kotu ta gaggauta daukan mataki domin hakurinsa na gab da karewa.
Ita kuwa Uwargidan Lawal, wato Saratu bata musanta korafin mijin ta ba sai dai ta bayyana wa kotu cewa ta na kin amince masa a gado ne a dalilin kin biyan ta bashin kudi da ya karba a wurinta har naira 20,000.
Ta roki kotu ta tilasta wa Lawal ya biya ta kudinta da ya karba.
Bayan ya saurare su alkalin kotun Dahiru Bamalli ya umurci Lawal ya gaggauta biyan Saratu kudinta sannan ita Saratu ta rika amince wa mijnta a duk lokacin da ya bukaci kusantarta.
Alkali Bamalli ya dage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu.