Jihar Filato za ta kafa rudunar jami’an tsaron jiha

0

Gwamnati jihar Filato za ta kafa rundunar jami’an tsaron mallakin jihar domin samar da tsaro a fadin jihar.

Gwamna Simon Lalong na Filato ya bayyana haka a taro yadda za a shawo rashin tsaro da ake fama da shi a jihar musamman a wannan lokaci.

An shirya wannan taro ne domin a samu hanyoyin da za a kawo karshen rashin zaman lafiyar da ake fama da shi a jihar.

Lalong ya yi kira ga mahalarta wannan taro da su tattauna sannan su samar da hanyoyin da za abi wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihar sannan da kuma da tsara hanyoyin da za a bi wajen daukar sabbin dakarun tsaro na jihar da gwamnati ta shirya.

“ Dama a can muna da kungiyoyin ‘yan banga a jihar da suka hada da Operation Rainbow, Early warning System da sauran wasu kungiyoyin sa kai.

Idan ba a manta ba a watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta umurci hukumar ‘yan sanda ta kasa ta horas da ma’aikatan da za su zama ‘yan sandan jihohi.

Hukumar ta kammala shiri tsaf sannan tana jiran umurin fara horas da ma’aikatan.

Lalong ya bayyana cewa zaman da kungiyar gwamnoni suka yi da shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa sun amince da yankin Arewa ta Tsakiya ta kirkiro da rundunar tsaro na sakai domin tsaron kasa.

Share.

game da Author