Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i JAMB ta bayyana cewa akalla dalibai 350,000 ne za su zana jarabawar gwaji na JAMB a fadin kasar nan.
Za a fara rubuta jarabawar ranar Talata sannan za a yi amfani da wuraren rubuta jarabawa 64 a kasan.
Shugaban hukumar Ishaq Oloyede ya sanar da haka a taron kaddamar da ginin tattance daukan daliban da za su shiga jami’a na JAMB da aka yi ranar Litini a Abuja.
An kashe Naira miliyan 230 wajen gina wannan wuri.
Hukumar ta kara jaddada cewa ba za a kara yawan ranakun yin rajistar wannan jarabawa ba.
An fara rajistan jarabawar ne ranar 13 ga watan Janairu sannan a gama ranar 17 ga watan Fabrairu.
Oloyede yace akalla dalibai miliyan 1.9 ne za su rubuta jarabawar JAMB sannan 200,000 ne za su rubuta jarabawar DE.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa an gina wajen tantance daukan dalibai masu shiga jami’a ne domin kawar da rashawa da cin hanci a wannan fanni.
Ya ce domin ganin haka ya tabbata ya zama dole ga kowa ce jami’a dake kasar nan ta shigar da sunayen daliban da zata dauka cikin jadawalin sunayen daliba ta.
Adamu ya ce za a dauki mumunar mataki kan duk jami’ar da bata yi haka ba.
Discussion about this post