Jagorancin El-Rufai ne ya sa muka yi nasara a saida kadarorin gwamnati a lokacin mulkin mu – Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya jinjina wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda ya bayyana cewa shine gogan da ya sa aka samu nasarar saida kadarorin gwamnati da gwamnatin sa ta yi a zamanin ya na shugaban kasa.

Obasanjo ya yabawa sannan yayi wa El-Rufai fatan alkhairi a wannan rana da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

El-Rufai ya cika shekara 60 a duniya.

” El-Rufai gogan aiki ne kuma ba ya shakkan tunkarar sa a ko da yaushe. Shine ya sa muka yi nasara a shirin mu na saida kadarorin gwamnati a lokacin mulkin mu.

Idan ba a manta ba El-Rufai ne shugaban hukumar saida kadarorin gwamnatin tarayya da aka kirkiro a lokacin mulkin Obasanjo a 1999 – 2007.

” Baya ga aikin wannan ma’aikata, El-Rufai ne ya gina babban birnin tarayya Abuja. Kowa shaida ne irin ayyukan da yayi a Abuja. Shine ya jaddada tsarin babban birnin.

” Yanzu kuma kaine gwamnan jihar Kaduna, wadda itace cibiyar Arewa. Kananan kana zabga aiki ba dadare ba rana. Wannan shine aka sanka da shi kuma ina kira a gareka da ka ci gaba da ayyuka domin mutanen jihar Kaduna da Arewa baki daya.

Ita ma kungiyar gwamnonin Arewa, karkashin shugabancin Simon Lalong, ya mika gaisuwar murnar zagayowar ranar haihuwar gwamna El-Rufai a madadin kungiyar, yana mai ya masa fatan Alkhairi da karin shekaru masu albarka.

Share.

game da Author