JA YA FADO JA YA DAUKA: Buhari zai ba gwamnan Kebbi dala milyan 100 daga kudin da ya taya Abacha jida

0

Wannan fa shi ake kira jaya fado, kuma ja ya dauke.

Kamar yadda Bloomberg ta buga, sun fallasa cewa Najeriya ta rattaba hannun yarjejeniyar da idan har ta tabbata, to za a bai wa Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, sama da dala milyan 100, daga cikin kudaden da ya taya tsohon shugaban kasa Sani Abacha jida su na kimshewa kasashen ketare.

An gano cewa da farko an rattaba wannan hannun tun cikin 2003, lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo, daga nan kuma aka sake sabuntawa da rattaba amincewa a yanzu da Buhari ke kan mulki.

A yanzu gwamnatin Buhari ta jajirce cewa ita ba ta goyon bayan karbo wadannan kudade daga hannun Bagudu.

Bagudu na daya daga cikin manyan gogarman Abacha, wanda ya rika amfani da kamfanonin bogi ya na dankara kudaden sata da sunan Sani Abacha, tsakanin 1993 zuwa 1998.

BAGUDU: Tsohon Dan Bursuna a Amurka
PREMIUM TIMES ta gano cewa Bagudu ya taba shafe watannin shida cur a kurkukun Amurka, cikin 2003.

An tsare shi ne a lokacin da Amurka ke kokarin damka shi ga gwamnatin Tsibirin New Jersey, domin amsa tambayoyi dangane da wasu kudaden sata da suka boye a cikin asusun wani kamfani mai suna Doraville Properties Corp, kamfanin da shi da Mohammed Abacha suka rika kimshe makudan kudade a ciki.

Yayin da Bagudu ya ga lallai Amurka za ta damka shi Tsibirin Jersey inda zai iya kwashe shekaru rututu a kurkuku, sai ya amince wa Amurka cewa “zai maida wa gwamnatin Najeriya dala milyan 163, idan aka yarda aka sake shi, kuma Jersey ta janye tuhumar da ta ke yi masa.”

Yarjejeniyar 2003 dai wata kotun Birtaniya ce ta amince da ita. To wani rahoto kuma da Bloomberg ta buga inda ta yanko wata ruwaya daga rubutun da Mai Shari’a John Bates na Washington D.C ya zartas, an ce Najeriya ba za ta gurfanar da Bagudu ba, matsawar ya maida mata wadannan dala milyan 163 din daga cikin wadancan kudade da suka rika jida a lokacin Abacha.

Illar Wannan Yarjejeniya Ga Gwamnatin Najeriya

Illar wannan yarjejeniya it ace Najeriya ta janye kenan daga bibiya, bin-diddigi da neman wani hakki a kan harkalla, dakasharama da lodin jida da jigilar kudaden da Atiku Bagudu ya rika yi daga Najeriya zuwa kasashen waje a zamanin Abacha.

Kenan Najeriya ta janye daga bibiyar sauran wasu kudaden da Amurka ke ta hakilon taimaka wa a maida wa kasashen Afrika dimbin kudaden na su da aka sata aka kimshe a waje.

Bayan an saki Bagudu a matsayin beli daga kurkukun Amurka, da ya dafe keya bai tsaya ko ina ba sai Najeriya ya dawo Najeriya. Ya yi mirsisi abin sa, ya shiga takara zama sanata, daga nan kuma ya yi takarar gwamna har sau biyu, duk ya yi nasara.

BAGUDU: Kowa Ya Samu Rana, Ya Yi Shanya
Mutumin da ya kwaci kan sa da kyar daga kurkukun Amurka, ya dafe keya ya bai wa yamma baya, ya sheko Najeriya, bayan ya dawo Najeriya sai ya shiga takarar siyasa, kuma ya ci sanata. Yanzu kuma ya na kan zangon sa na biyu a matsayin gwamnan jihar Kebbi.

Su ne manyan shiyya a cikin jam’iyyar APC, jam’iyyar kawo canjin murkushe cin hanci da rashawar da ake zargin an tabka a zamanin PDP.

Ya murje idon sa da toka, ya maka gwamnatin Najeriya kara a cikin 2018, ya na zargin ta karya yarjejeniyar 2003 da aka kulla.

Ganin haka, sai gwamnatin Najeriya, wadda shugaban ta Buhari da Bagudu, duk ’yan Jam’iyya daya ne, APC, suka sake yi wa waccan jarjejeniya kwaskwarima.

A yanzu abin da suka rattaba shi ne za a maida wa Najeriya jarin kamfani na dala milyan 155. Ita kuma za ta biya Bagudu da sauran ’yankirin sa dala milyan 106, kwatankwacin naira bilyan 38.5.

Haka dai Bloomberg ta buga, kuma ta ce wani alkali ne ya ruwaito haka a birnin Washington na Amurka.

Amurka da Ingila Sun Rufe Kofar da Najeriya Za Ta Sakar wa Bagudu Kudaden
Bloomberg ta ce har yanzu ba a saki kudaden ga Najeriya da kuma shi kan sa uban gayya, Bagudu ba, saboda Amurka ta umarci Birtaniya kada ta saki kudaden.

Duk da haka, Najeriya ta ce ita dai ta amince da yarjejeniyar Bagudu da suka kulla cikin 2018. Kuma babu ruwan ta da taimaka wa Amurka bibiya ko shiga rikicin ta da Bagudu.

Bloomberg ta ruwaito cewa Amurka ta ki yarda a bai wa Bagudu ko sisi daga cikin kudaden, domin idan aka yi haka, to an yi wa kudaden sata abin da ake kira ‘ja ya fado, ja ya dauke’ kenan.

PREMIUM TIMES ta yi iya kokarin ta Ministan Shari’a Malami ya yi magana, amma bai ce komai ba.

Shi ma Gwamnan Kebbi an yi ta kokarin ya ce wani abu, shi ma ya ki cewa kullum.

Tarihin Dawo Da Kudaden Satar Abacha
An fara jidalin kokarin dawo da kudaden da aka sace zamanin Abacha, tun a cikin 1999, bayan Obasanjo ya hau mulki.

Cikin watan Afrilu, 2002, iyalan Abacha sun maido dala bilyan 1 daga kasar Switzerland.

An yi yarjejeniya da iyalan Abacha cewa an yarda su rike dala milyan 100, amma su bayar da sauran. Gwamnatin Najeriya a lokacin kuma ta janye tuhumar da za a yi wa dan sa Mohammed Abacha a kotu.

Haka dai jaridar New York Times ta buga a lokacin.

Cikin 2006 kuma kasar Switzerland ta sake maido wa Najeriya da dala milyan 723. Sai dai kuma a lokacin, Kungiyar Sa-ido ta Transparency International ta bayyana cewa an yi kumbiya-kumbiya wajen sanin takamaimai da tartibin yadda aka yi da kudaden.

Switzerland Ba Ta Amince Da Shugabannin Najeriya Ba

“Zargin an yi walankeluwa da wasu kudaden da ta maido wa Najeriya cikin 2006, sai Switzerland ta nemi goyon bayan Bankin Duniya a cikin 2018, aka kulla yarjejeniyar cewa cikon wasu dalalo milyan 322 da za ta maido wa Najeriya, za ta damka su ne ga Bankin Duniya (World Bank), shi kuma zai zauna da mahukuntan Najeriya su fada masa abinda za a yi musu da kudaden na raya kasa.”

Haka dai Tranparency International ra ruwaito an yi.

Ko kwanan nan dai an sake karbo dala milyan 308 daga cikin burbushin sauran canjin da suka rage ba a karasa karbowa ba.

Wadannan na baya-bayan nan, an kwato su ne daga cikin wadanda Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya yi jigilar arcewa da su kasar Tsibirin Jersey ne a lokacin mulkin Abacha.

Kungiyar Transparency International dai ta kiyasta cewa Abacha ya saci kimanin dala bilyan uku zuwa biyar ya kimshe a kasashen waje.

Share.

game da Author