Babban Lauya Kanu Igabi ya sake garzayawa Kotun Koli, rungume da tulin korafe-korafen hukuncin Kotun Koli da aka tsige wanda ya ke karewa, tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.
Kotun Koli ta tsige Ihedioha na PDP ranar 14 Ga Janairu, ta maye gurbin sa da dan takarar APC, wanda ya zo na hudu, Hope Uzodinma.
Wannan hukunci ya bai wa dimbin jama’a mamaki, kama daga masana shari’a zuwa wasu daban-daban.
Babban Lauya Kanu Igabi ya dira Kotun Koli tare da sake shigar da karar neman a sake duba shari’ar, domin a cewar sa, kotun ta tabka babban kuskure wajen yanke hukunci.
Dama kuma ita ma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ta na nan a matsayin ta cewa Uzodinma bai ci zabe ba. Don haka ba ta gamsu da yadda Kotun Koli ta tsige Ihedioha, ta dora Uzodinma na APC ba.
Dukkan alkalan Kotun Kolin su bakwai dai ne suka amince da tsige Ihedioha da kuma maye gurbin sa da Uzodinma.
Sun ce INEC ta aikata ba daidai ba da ta kai lissafa sakamakon zaben wasu rumfuna 388.
Don haka sai ita Kotun Koli ta yi amfani da sakamakon zaben da ta ce INEC ba ta lissafa da su ba, ta ce Uzodinma ya fi kowa samun kuri’u masu yawa.
Sai dai kuma babban lauya Kanu Igabi ya ce Uzodinma da lauyoyin sa sun yaudari Kotun Koli da sakamakon zabe na bogi, wanda ta yi amfani da shi har ta yanke danyen hukunci.
Yayin da lauyoyin Ihedioha suka hada adadin kuri’un da Kotun Koli ta ce Ihedioha ya samu, to sai ya zama yawan kuri’un da aka kada sun zarce yawan wadanda INEC ta tantance.
INEC ta tantance kuri’u 731,485, amma lissafin da Kotun Koli ta yi ta kara wa Uzodinma kuri’u har ya zama na daya alhali shi ne na hudu, sai ya nuna an jefa kuri’u har 823,743.
A kan haka ne Ihedioha ya koma Kotun Koli, ya ce ba ta yi masa adalci ba. Don haka ya na nema ta mayar masa da kujerar sa.
Dama bayan yanke hukunci an yi ta mamakin yadda Kotun Koli ba ta yi cikakken jawabin ko kuri’u nawa kowane dan takara ya samu daga cikin wadancan rumfuna 388 ba.