Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ta rage yawan jam’iyyun siyasa dake Najeriya daga 92 zuwa 18.
Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.
Mahmood ya ce hukumar sa ta yi haka ne bisa damar da tsarin mulkin Najeriya ya ba ta na iya yiwa jam’iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam’iyyun da suka ga ya kamata a soke ko dan rashin tasiri ko kuma a wani dalili da doka ya bata dama.
Bayan nan ya kara da cewa hukumar ta yi kyakkyawar dubi da nazarin tasirin da jam’iyyu suka yi da irin rawar da suka taka a zabukan da aka yi a akasar nana har da wadanda aka yi a abaya-bayannan wato sake zabe da kuma cike gurbi.
” Hukumar INEC ta lura cewa jam’iyyu 16 ne suka cika ka’idojin da tsarin mulkin Najeriya ya bayyana da ya basu damar ci gaba da aiki a matsayin jam’iyya a kasar nan.
Sai dai kuma ya ce akwai jam’iyyu biyu da kotu ta bada dama su ci gaba da zama a matsayin jam’iyyu a kasar nan. Jam’iyyun su ne Jam’iyyar Actions People Party APP, har yanzu ana shari’ar karar da jam’iyyar ta shigar tana na kada hukumar INEC ta soke zamanta a matsayin jam’iyyar.
Saboda haka APP za ta ci gaba da zama jam’iyya har sai kotu ta yanke hukunci akan shari’ar dake gaban ta.
Sai kuma jam’iyyar (Boot Party) wacce ita ma umarnin kotu ne hukumar tabi.


Discussion about this post