Hukumar NFIU ta kaddamar da manhajar dakile harkallar kudade ta intanet

0

Hukumar Bankado Harkallar Kudade, National, Financial Intelligence Unit (NFIU), ta kaddamar da wata manhajar intanet domin zamanantar da aikin ta.

Wannan manhaja an sa mata suna Manhajar Tattara Bayanan Laifuka, wato CRIMS.

An kaddamar da wannan manhaja a ranar Laraba domin aiki da ita a kowane bangaren binciken laifuka ta na’urori da wayoyin android da ios a kowace hukumar binciken zamba da harkallar kudade a kasar nan, wato CRIMS.

Za a rika amfani da wannan manhaja, wato ‘applicarion’ wajen zakulo duk wasu bayanan sirri na harkalla a cikin wayoyin wadanda ake zargin sun tabka wata harkalla ko laifi.

Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ne ya kaddamar da manhajar, kuma ya raba ta ga dukkan hukumomin ayyukan da suka shafi dakile zambar kudade a wurin kaddamarwar.

Ya yi kira da su yi amfani da manhajar wajen likawa da had a ta da dabarun killace dukkan gwajin jinin duk wani mai laifi, ta yadda za a rika tattara bayanan duk wasu ayyuka ko ta’asar zamba da suka kitsa.

Kafin nan sai da Shugaban Hukumar NFIU, Modibbo Hamman Tukur ya bayyana cewa manhajar CRIMS ta yi amfani har ga Manyan Masu Shari’a, Ma’aikatar Shari’a, Sojoji, Tsaro da kuma Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) da kuma DSS.

“Za a kafa wannan manhaja ga dukkan ofisoshin ‘yan sanda a kasar nan, har da ofishin Shige-da-fice da bangarorin jami’an kwastan.” Inji Tukur.

A wurin kaddamar da wannan manhajar tattara bayanan laifuka, wato CRIMS, dukkan shugabannin bangarorin hukumomin tsaro sun turo wakilan su sun wakilce su.

Share.

game da Author