HAUSA BA DABO BACE: Bahaushe Mai ‘Ya’ya Da Yawa!

0

‘Yan siyasa. ‘Yan kwallo. ‘Yan kasuwa. ‘Yankama. ‘Yan kokawa. ‘Yan gambara. ‘Yan caca. ‘Yan jagaliya. ‘Yandaudu. ‘Yan fashi. ‘Yan wala-wala. ‘Yan bori. ‘Yan dambe. ‘Yan takife. ‘Yan Izala. ‘Yan Darika. ‘Yan Kadiriyya. ‘Yan Tatsine. ‘Yan Tijjaniyya. ‘Yan Shi’a. ‘Yan Kala-kato.

‘Yan sharo. ‘Yan mata. ‘Yan bumburutu. ‘Yan cuwa-cuwa. ‘Yan ci-rani. ‘Yan gudun hijira. ‘Yan alewa. ‘Yan kwadago. ‘Yan barema. ‘Yan kiya-kiya. ‘Yan zamani. ‘Yan ga-ruwa. ‘Yansambo. ‘Yan kurkutu. ‘Yan amshi. ‘Yan rawa. ‘Yan fito.

‘Yanruwa. ‘Yan birni da ‘Yan kauye.’Yankoli. ‘Yan tasha. ‘Yan gambara. ‘Yan kacakaura. ‘Yan sanda. ‘Yan Kato-da-gora. ‘Yan kwaya. ‘Yan wiwi.

‘Yan giya. ‘Yan sumogal. ‘Yan sane. ‘Yan bindiga. ‘Yan samame. ‘Yan cori. ‘Yan kiri. ‘Yan kamasho. ‘Yan Boko Haram. ‘Yan Alka’ida. ‘Yan bori. ‘Yan duba. ‘Yan farauta. ‘Yan Zariya. ‘Yan’awaki, ‘Yan fim da ‘Yan jarida.

‘Yan aljanna, ‘yan wuta. ‘Yan yaga-riga. ‘Yan su. ‘Yan kabalu. ‘Yan sadalu. ‘Yan sama jannati. ‘Yan santsi. ‘Yan tabo. ‘Yan ‘Yan NEPU. ‘Yan ba-ruwan-mu. ‘Yandoka. ‘Yan tsurku. ‘Yan buyagi. ‘Yan iska. ‘Yan baranda.

‘Yan Kwankwasiyya. ‘Yan Buhariyya. ‘Yan maza. ‘Yan duniya. ‘Yan kwanta-kwanta. ‘Yan makaranta. ‘Yandoka. ‘Yan baka. ‘Yan babule. ‘Yan Salafiyya. ‘Yan Fityanu. ‘Yan raraka. ‘Yan Hisbah.

‘Yan KAROTA. ‘Yan Agaji. ‘Yan acaba. ‘Yan bursuna. ‘Yan sholisho. ‘Yan kalare. ‘Yan a-mutu. ‘Yan kunar-bakin-wake.

‘Yan amshin-Shata. ‘Yan maula. ‘Yan A Daidaita Sahu. ‘Yan Majalisa. ‘Yan kungiya. ‘Yan gudubale. ‘Yan kwalisa. ‘Yan burazas. ’Yanruwa. ’Yan ruwa-ruwa. ’Yan kwangila. ’Yan kakuduba.

Share.

game da Author