‘Yan jagaliyar siyasa sun yi wa shugaban jam’iyyar APC na jihar Kwara Bashir Bolarinwa ruwan duwatsu a hanyar zuwa karamar hukumar Moro ranar Talata.
Hasalallun matasan da suka kai 20 sun far wa jerin gwanon motocin Bolarinwa a kauyen Shao inda suka rika yi masa ihu suna jifa suna yi masa kirarin “Bolarin Barawo”.
Bolarinwa ya gamu da wannan tashin hanakali ne a hanyarsa ta zuwa Moro, wajen sasasnta wasu ‘ya’yan jam’iyyar da suke gaba da juna.
Gwamnan jihar Abdulrasaq Abdulrahaman ya yi tir ta wannan abu da aka yi wa shugaban jam’iyyar yana mai cewa gwamnati baza ta yi kasa kasa ba wajen hukunta duk masu neman tada zaune tsaye a jihar.
Abdulrahaman ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun cafko wadanda suka shirya wannan ta’addanci ga shugaban jam’iyyar.
Discussion about this post