Hukumar EFCC a Kano ta damke Mukhtar Ishaq, Kwamishinan Ayyukan Musamman na Gwamna Abdullahi Ganduje.
Ana tuhumar Ishaq da yi wa naira milyan 86 rub-da-ciki, a lokacin da ya ke Shugaban Karamar Hukumar Birni da Kewaye (Kano Municipal0.
Kakakin Yada Labaran EFCC na Riko, Tony Orilade ya bayyana wannan kamu da aka yi wa Kwamishinan Ganduje a Kano.
Orilade ya ce an kama Ishaq ne bayan da hukumar ta samu korafi daga wani cewa kwamishinan ya yi sama-da-fadin kudaden ayyukan raya al’umma, har naira milyan 86.
Takardar korafin ta bayyana cewa a lokacin da Ishaq ya ke Shugaban Karamar Hukumar Birni, ya cire naira 30,000 daga asusun kowane kansila, ba tare da shawartar su ba.
‘Kwamishinan ya kuma maida wani fili na Firamare ta Kofar Nasarawa zuwa kantina. Sannan ya rika sayar da kowane a kan naira milyan 10. Duk wanda ya sayar kuma sai ya watsa kudin cikin aljihun sa.” Haka EFCC ta bayyana a sanarwar manema labarai da ta fitar.
EFCC ta ce da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da Ishaq a gaban kotu.
Idan ba a manta ta, a Kano an yi rudanin zargin kama Gwamna Abdullahi Ganduje ya na loda daurin damman daloli aljihun sa.
Rudanin ya kai ha kafa kwamitin bincike na Majalisar Jihar Kano.
Ba a dai gurfanar da Ganduje kotu ba, saboda ya na da rikar kariya a matsayin sa na gwamna.