Mutanen jihar Legas sun waye gari a ranar Asabar cikin fara aikin dokar hana acaba da Keke Napep a jihar da kananan hukumomin jihar.
Mutane da dama sun shiga halin ha-ula-I a dalilin fara aikin wannan doka.
Mata musamman ‘yan kasuwa sun koka kan yadda harkokin kasuwancin su ya tsaya cak a jihar a dalilin wannan doka.
Yanzu gashi mun fada cikin mummunar matsala a jihar.
Sai dai wasu sun yaba wa gwamnatin jihar ne bisa wannan doma da ta saka na hana masu acaba da keke Napep aiki a fadin jihar.
“Ba za ka san illar masu baburan acaba ba, har sai hatsarin da su ke haddasawa ya ritsa da kai, ko wani na ka. Ko kuma idan ka je asibitocin ka ga jama’ar da suka ji wa ciwo kwance ranga-ranga. Sannan za ka yaba wa gwamnati a kan hana su haya da aka yi.”
-Wata mai suna jibike, a hirar ta da PREMIUM TIMES, ranar Lahadi, a Legas.
Kafafen yada labarai sun nuna yadda ake lodin baburan acaba daga Legas, cike da tireloli wadanda ke makare da matasan Arewa, ana jigilar su zuwa Arewa.
Ko a Arewan ma wasu jihohi da dama na kokarin hana wannan sana’a.
Idan ba a manta ba, a babban birnin tarayya, Abuja ma an hana kabu-kabu tun a karshen shekarar 2019.

Discussion about this post