Sanatoci sun bayyana dalilin da ya sa suke yabawa da jinjina wa wasu kasashe, kamar su Rwanda, saboda irin kyakkyawan tsarin tafiyar da ayuukan gwamnati da suke yi.
Amma maimakon su yaba wa Najeriya, sun bayyana tsarin kasafin kudin kasar nan cewa cire ya ke da hauma-haumar banzatar da makudan kudade.
Sun yi kaca-kaca da Najeriya ne, bayan da Sanata Stella Oduah, ’yar PDP daga Jihar Anambra, ta kawo hanzarin bukatar a zartas da kudirin da zai tilasta gwamnatin Najeriya ta fito ko ta kafa wani muhimmin Tsare-tsaren Tafiyar da Kasafin Kudi a kan Muhimman Ayyukan Rayawa da Inganta kasa.
Wannan neman kudiri ya zo ne a daidai lokacin da daidaikun jama’a a kungiyoyin sa-ido ke ragargazar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari cewa yawancin kasafin kudin da ma’aikatun gwamnatin sa suka gabatar da Majallisa, duk cike suke da azuraren makudan bilyoyin kudade da aka cusa a cikin kasafin.
Mutane da yawa sun ce ayyukan haramben da ‘yan majalisa suka cusa a cikin kasafin kudin, ba wani abu ba ne, sai dai kawai hanya ce ko wani bututun da za a zurara makudan kudade, sai a tara can gaba a kwashe.
A duk shekara ana cusa wadansu kwangiloli wadanda ke da alamar tambaya. Ko cikin kasafin 2020 ma sai a Majalisa ta yi karin aringizo, amma Buhari bai yi korafi ba, sai ma jinjina wa majalisar da ya yi.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Majalisa ta yi aringizon ayyukan naira bilyan 264, wadanda ake zargin cewa karkatar da kudin za a yi ta wasu hanyoyi daban.
Sanata Oduah ta ce sama da shekaru 20 kenan gwamnatin Najeriya ta na fito da shirye-shiryen Inganta Tattalin Arziki wato development plans, amma har yau babu wani abin a zo a gani da aka tsinana.
“Idan fa babu wani sahihin tsari ko shirin inganta kasa, to abin da aka tsara ko aka gina, rushewa zai yi.
Daga nan sai Sanatoci suka rika tashi daya-bayan-daya su na bayanin yadda gwamnatin Najeriya ba ta bisa wata akiblar da za a iya yin dogaro da ita, har kasar ta bunkasa ta zama daya daga cikin manyan kasashe 20 a kasashen masu tasowa.
Wasu daga cikin wadanda suka yi bayani, sun hada da Mathew Urhoghide, wanda ya ce Najeriya tafiyar-kura kawai ta ke yi, saboda ba a dora shirin inganta tattalin arzikin kasa a kan mizani daya da kasafin kudin kasa.
“Idan mai hankali zai tsaya tsaf ya dubi irin kudaden da za a kashe a wasu bangarorin da ba su da wani tasiri a kan inganta kasa da al’umma, mutum zai ga kamar ba mu ma san abin da za mu yi da kudi ba, sahi ya sa muke tafiya cikin harankazama.
“Inda kuma za ka kara gane cewa ba mu da wata alkibla, sai ka ga idan an zo babun tsara wani shiri, to mu daban muke. Komai a cikin sirri da nuku-nuku za a yi shi.”
Shi ma Sanata Elisha Abbo daga Jihar Adamawa, da sauran wasu sanatocin suk sun bayyana irin ta su damuwar.
Sun ci gaba da cewa duk wani abu da Najeriya za ta tsara, tun daga kiwon lafiya, harkokin ilmi, noma, masana’antu da sauran su, duk cike da harmagaza, hauma-hauma, hauragiya da harambe ya ke.