Atoni Janar din jihar Kaduna Aisha Dikko ta bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kalubalanci hukuncin Kotu a Kaduna da ta saki ‘yan shi’a 91.
Dikko ta ce dalilan da maishari’a Hajaratu Gwadah ta bada na sakin wadanda ke tsaren bai gamsar da su ba.
A ranar Juma’a ne kotu a Kaduna karkashin maishari’a Hajaratu Gwadah ta yanke hukuncin sakin ‘yan shi’a 91 dake tsare tun a shekarar 2015.
Hajaratu ta ce hujjojin da gwamnatin Kaduna ta mika gaban kotu basu yi tasiri ba, a dalilin haka ta yi watsi da da su sannan ta umarci da aka sake su da gaggawa.
Sai dai awowi kadan bayan yanke wannan hukunci gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa lallai ba za ta amince da wannan hukunci ba, za ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
A doguwar takarda da Kwamishinan shari’a ta jihar Aisha Dikko ta raba wa manema labarai, ta ce hujjojin da suka mika masu karfi ne kwarai sai dai idan kotun ba su bisu dalla-dalla ba.
” Ko a shekarar 2015 bayan arangamar da ‘yan shi’a suka yi Tawagar Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai, an kama akalla mutane 90 kuma dukkan su mun mika su ga ‘yan sanda tun a wancan lokaci.
” Sannan kuma mun mika abubuwan da muka kamasu da su wanda suka saba wa doka kuma duk mun mika su ga ‘yan sanda kamar yadda doka ta ce. Sannan kuma har da masu bada shaida duk sun bayyana a gaba kotu a lokacin da take zama.
Har yanzu dai Shugaban kungiyar Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zeenat na tsare aa hukumar SSS.
Discussion about this post