Gwamnatin Edo ta mika wa Shugabannin ‘Yan Sanda da DSS sammacin kama Oshiomhole

0

Gwamnatin Jihar Edo ta ce ta bai wa Sufeto Janar da Babban Daraktan DSS sammacin kama Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, saboda karya dokar da gwamnati ta kafa ta dakatar da taron siyasa.

Mataimakin Gwamna Philips Shuaibu ne ya bayyana haka a Abuja, a ranar Litinin, Jim Kazan bayan kammala taron gwamnoni da aka yi a kan Madafun Kyakkyawan Shugabanci.

Shuaibu ya ce Gwamnatin Edo ta shirya mika sammacin hannu-da-hannu ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu da kuma Babban Daraktan SSS, Yusuf Bichi.

“Na yi takakkiya zuwa Abuja ne domin na damka takardar sammacin kama Shugaban APC, Adams Oshiomhole ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da kuma Shugaban SSS, saboda ya karya dokar hana taron gangamin siyasa.

“Gwamnatin Jiha ta hana taron gangami, Sufeto Janar ya hana taron gangami. Amma shi Oshiomhole gani ya ke yi kamar ya fi karfin doka.

“Idan har gwamnati za ta kafa doka amma Oshiomhole ya karya, to idan jam’iyyar adawa ta yi na ta taron, babu yadda za a yi da ita kenan, tunda ta na da hujjar cewa wani ma ya yi, ba a yi komai a kai ba.

Shuaibu ya ce bai kamata a zura ido fitintinu na tashi ba a duk lokacin da Oshiomole ya shiga Edo.

“Ai shi ma da ya na gwamna ya kafa doka, ba a karya ba. To bai yiwuwa don ya sauka daga gwamna shi dawo ya ka karya doka, mu kuma mu kasa taka masa burki.”

Tilawar Rikicin Obaseki Da Oshiomhole

Kwatagwangwamar turnukun rikicin siyasa sai kara dagulewa ya ke tsakanin Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki da kuma tsohon gwamnan da ya gada, kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa a yanzu, Adams Oshiomhole.

A wani kurari da hargagin barazana da Mataimakin Gwamnan Edo, Phillips Shaibu ya yi, za a iya cewa an saka wa Oshiomhole takunkumin shiga jihar, bayan da Shaaibu ya ce kada Oshionhole ya kuskura ya shiga jihar ba tare da neman iznin Gwamna Obaseki ba.

A daya bangare dai sabbin zababbun Mambobin Majalisar Dokokin Edo sun ce akwai wata makarkashiyar da ake kullawa da nufin a kashe Oshiomhole idan ya shiga Edo.

Shaibu ya yi wannan jawabi kan Oshiomhole a Karamar Hukumar Egor, a lokacin da ya je tarbar sake karbar Shugaban Karamar Hukumar Egor, Edgar Ogbemudia bayan dakatarwar da aka yi masa.

“Tunda mun fahimci duk inda Oshiomhole ya shiga a cikin jihar nan sai an tayar da hargitsi, sai gwamnati ta yanke shawarar cewa kada ya kara shigowa ba tare da neman izni daga wurin Gwamna Obaseki ba.”

“Bai yiwuwa ya ci gaba da shigowa jihar Edo a kullum ya na tayar da hankali, rikici da kuma fitintinu. Edo jiha ce mai zaman lafiya, kowa ya sani.

Tuni dai ake ci gaba da watsa wani bidiyo a shafukan tweeter, mai dauke da mataimakin gwamnan ya na wannan jawabin.

Shaibu wanda ya yi magana da ‘pidgin English’, ya ce Oshiomhole ne da kan sa ya ce su yaki siyasar ubangida a lokacin da ya ke gwamna.

Ya ce Oshiomhole bai yarda wani babban dan siyasa ya juya shi ba. Don haka babu wani dalilin da zai sa shi kuma bayan ya sauka ya ce lallai tilas sai ya juya Gwamna Obaseki.

Obaseki dai shi ya gaji Oshiomhole bayan saukar sa. Sai dai kuma sun raba hanya, kowa ya kama gaban sa, bayan da gwamna ya yi korafin cewa Oshiomhole na neman ya rika juya shi kamar waina.

“Ahaf, shi ya dauka mu wasu sakarkaru ne? To yanzu fa lokaci ya yi da za mu nuna masa cewa mun kware sosai a kan darasin da ya kowa mana, wato darasin bijire wa siyarar ubangida.”

Ya ci gaba da bai wa dimbin masu sauraro labarin yadda ya koya musu bijirewa ga siyasar katsalandan ta ubangida, ya na cewa, “tun mu na yaran sa ya koya mana cewa idan mun girma, kada mu yarda wani ya zo ya nuna mana wai mu yara ne. Ehe!

“Don haka yanzu ka mu nuna masa mun girma, ba kuma za mu yarda ya dawo da kan sa ba ya nemi ya nuna mana wai mu kananan yara ne ba.

“Shin jama’a wannan fada da mu ke yi, ba da wani gogarman da ke neman zama ubangidan gwamna da gwamnati mu ke yi ba? Za mu bari ya zo ya maida Edo a hannun sa?”

Duk tambayar da Mataimakin Gwamna ya yi, said dimbin jama’a sun amsa masa da babbar murya, mai nuna alamar su na jin dadin wankin babban bargon da ya ke yi wa Oshiomhole.

“Oshiomhole ya Isa ya je Kano ko Kaduna ya ce zai yi gangamin APC ba tare da ya nemi izni daga wurin Ganduje ko El- Rufai ba?”

Jama’a duk su ka dauka gabadaya suka ce, “‘a’a”.

PREMIUM TIMES ta tambayi kakakin yada labarai na mataimakin gwamna, ko ba ya ganin kalaman da Shaibu ya yi za su iya haddasa wata rigimar? Ya ce ko kadan, abin da yi gargadi ne ga Oshiomhole domin ya daina haddasa rigima a Edo, tunda shi a yanzu ba gwamna ba ne.

Share.

game da Author