Mataimakin shugaban sashen kula da dazuka na ma’aikatar muhalli Tiamiyu Oladele ya shaida cewa gwamnati za ta shuka itatuwa miliyan 30 a cikin wannan shekara na 2020 a kasar nan.
Oladele ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Litini.
Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ware kudade domin shuka itatuwa miliyan 30 sannan ma’aikatar muhalli ta kammala shiri tsaf domin ganin haka ya tabbata.
“Ma’aikatar mu ta shirya ta shuka itatuwa miliyan 30 daga cikin miliyan 35 a cikin wannan shekara sannan ma’aikatar za ta raba irin itatuwan ga manoma da mutane domin shukawa a gonaki da wurare mafi kusa.
Ya ce ‘yan katako da masu yin gawayi na cikin mutanen dake sare itatuwa ba tare da suna shuka wani ba.
“Gwamnati zats co gaba da wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da sare itatuwa ga muhalli da amfanin da barin shi ke yi wa kiwon lafiyar mutane.
“Za kuma a kafa kwamiti wanda a ciki akwai wakilan ma’aikatan muhalli, ‘Yan katako da masu yin gawayi wanda za su sa ido wajen ganin an hana mutane sare itatuwa ba tare da izini ba.
A watan Yuli 2018 ne mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara kan hana zaizayar kasa da kwararowar hamada Mansur Kaura ya bayyana cewa gwamnatin ta shuka itatuwa 24,000 a wasu kananan hukumomin jihar domin kawar da matsalar kwararowar hamada da ake fama dashi.
Kaura ya ce “Gwamnati ta shuka itatuwa 1,000 a kananan hukumomi 14 da wasu 10,000 a kananan hukumomi shida akan Naira miliyan 10.
Gwamnati ta dauki wannan mataki domin ta kare garuruwan jihar daga matsalolin zaizayar Kasa da matsalolin kwararowar Hamada.