Ministan kimiya da fasaha Obonnaya Onu ya bayyana cewa gwamnati za ta kara karfafa matakan koran kudan tsando a kasar nan.
Onu ya fadi haka ne a ziyarar da ya kai hukumar gudanar da bincike kan cutar da kudan tsando ke haddasawa (NITR) dake Kaduna.
Ya ce ya zama dole gwamnati ta tsara hanyoyin da zasu taimaka wajen hana yaduwar cutar da wannan kuda ke haddasawa wato ‘Sleeping sickness’ idan har ana son samun ci gaba da samun nama mai tsafta a Najeriya.
Ya yi kira ga hukumar da ta zage damtse wajen kirkiro hanyoyin da za abi domin korar wannan kuda daga kasar nan.
Onu ya kuma ce hukumar ta shirya gudanar da bincike kan hanyar kawar da sauro domin maganin zazzabin cizon sauro.
A nashi tsokacin shugaban hukumar Augustine Igwe yace hukumar za ta gina sabbin wuraren yin gwaji da gudanar da bincike domin wadanda take da su sun tsufa sannan hukumar za ta gina wuraren yin gwajin cutar ‘Sleeping sickness’ a wuraren da aka fi fama da cutar a kasar nan.
Sleeping sickness cuta ce dake kama mutum da dabbobi musamman shannu da dawakai wanda idan ba a gaggauta neman magani ba ke kashe dabba cikin lokaci kalilan
Bayanan kungiyar kiwon lafiya (WHO) ya nuna cewa mutum na iya kamuwa da wannan cuta idan kudan ya cije shi sannan yawan kusantan dabbar dake dauke da cutar, cin naman dabar da ya kamu da cutar na sa a kamu da cutar.
Alamomin cutar a jikin dabba sun hada da zazzabi, yawan barci,rashin iya cin abinci da mutuwa.
A jikin mutum kuwa sun hada da zazzabi, yawan barci da rana da rashin samun barci da dadare, ciwon kai, ciwon gabobbin jiki da sauran su.
Sannan idan cutar ya dade a jikin mutum yakan shafi kwakwalwa inda daga nan sai mutuwa.
WHO ta ce a gaggauta zuwa asibiti da zaran an kamu da wannan cuta domin yin haka zai taimaka wajen warkewa daga cutar.
Sannan a tsaftace muhalli musamman na dabbobi tare da amfani da maganin koran kwari.