Gwamnati za ku yi wa bara, ba mutanen gari ba – Kiran Sarki Sanusi ga mabarata

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll, ya nemi mabarata su rabu da sauran jama’a, su maida hankali wajen yin barace-baracen su ga gwamnati.

Sarki ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke bayani wurin Taron Kungiyar Mahaddatan Alkur’ani na Kasa da aka shirya a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

An shirya taron ne da zimmar kawo gyara da kuma lalubo hanyoyin tsaftace almajirci.

Daga nan ya yi kiran iyaye su daina tura yaran su wasu garuruwa da sunan tafiya almajirci.

Ya ce kamata ya yi kowane uban yaro ya ya bar dan sa a gaban sa, a rika koyar da shi a hannun malaman da ke kusa da su a cikin garin.

Sarki ya kara da cewa idan ma tura yaro karatu zuwa wani gari ya zama tilas ga iyaye, to sai uba ya tabbatar ya hada wa yaron duk wani hakkin da ya kamata ya ba shi, wanda zai dauki nauyin ciyar da dan na sa, tufatar da shi, kai da ma dukkan sauran dawainiyar yau da kullum.

Ya ce babu yadda za a yi ka tura dan ka karatu wani gari babu kula, kuma a yi tunanin ba zai yi bara ba. Ya ce hakan ba daidai ba ne, kuma bai dace ba.

Daga nan ya kawo aya da hadisai masu nuna cewa mabarata a ranar alkiyama za su tashi fuskokun su babu fata.

Sai ya kara yin kira ga iyaye maza su gode wa Allah da ya albarkace su da ‘ya’ya da mata, ta hanyar kulawa da su duka, ba wai su bar ‘yan su ko su tura su barace-barace a cikin al’umma ba.

“Musulunci bai yarda da barace-barace ba. Idan ma har tilas sai ka yi bara, to gwamnati ya kamata ka yi wa, ba al’umma za ka rika bi ka na rokon ta ba ka ba.

Sana’ar Faskare Ta Fi Bara Albarka

“Har gara ka tafi ka na sana’ar faskare ya fi mutunci da kima fiye da ka rika bin jama’a ka na barace-barace.

“Jama’ar gari ko makautan ka da dangi da sauran abokan arziki, duk za su iya ba ka tallafi ko wani agaji idan bukatar hakan ta taso. Amma ba bin su ake yi ana ta yi musu barace-barace ba.

“Don haka duk wanda ya ce bara ba aibi ba ce, ko ya ce maka Musulunci bai hana bara ba, to ya na yaudarar ka ne kawai.”

Daga nan ya yi kira ga gwamnati ta kara bijiro da shirye-shiryen tallafa wa masu karamin karfi a cikin al’umma.

Sauran wadanda su ka yi jawabai a wurin taron a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, sun hada da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar lll, sai kuma tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima da kuma Mataimakin Gwamnan Jigawa, Umar Namadi.

Share.

game da Author