Wata mahaukaciyar guguwa da aka yi tare da ruwan sama mai karbi, ta haddasa wa jirgin British Airways kasa sauka filin jiragen Heathrow na Landan.
Al’amarin ya faru a ranar Lahadi da ta wuce. Jirgin wanda ya tashi daga Abuja, ya isa London ana kwada ruwan sama da mahaukaciyar iska.
Matukin jirgin ya yi kokarin sauka da farko. Jirgin ya dira kasa, sai ya fara galauniya da tangadi da tangal-tangal. Hakan ya sa tilas ya kara cirawa sama, sai da ya kewaye filin gaba daya ya na shawagi a sama.
An nuno shi a Yutube ya na kokarin sauka da shawagi. Kuma an tabbatar akwai ‘yan Najeriya da dama a ciki.
Wani mai suna Charles Okonkwo da abin ya ritsa da shi, a rubuta a shafin sa ba Facebook cewa, “tun da na ke ban taba firgita kamar a lokacin ba.”
Guguwar mai suna ‘Storm Ciara’, ta zo da ambaliya mai karfi sosai a fadin Ingila, kuma ta haddada barna da ambaliya mai yawa.
Gidaje sama da 20,000 sun shafe Asabar da Lahadi babu wutar lantarki.
Al’amurran sun tsaya cak a wurare da garuruwa da dama. Rahotanni sun ce harkokin sufuri sun tsaya, haka zirga-zirgar jiragen kasa.
Guguwar ta rika gudun kusan milyan 60 har zuwa 80 a cikin sa’a daya. Kuma ruwa ya mamaye wurare da gidaje masu yawa.
Yau din nan kuma Tarayyar Turai ta bada sanarwar cewa za a samu ruwan sama mai yawan gaske a Turai a wannan daminar.
A kan haka ne ta yi sanarwar cewa tun yanzu a yi shirin fuskantar gagarimar ambaliya, kasnlancewa ruwan da zai karu a bana zai kai kashi 35 bisa 100 na wanda ake samu a kowace damina.