GOBARA DAGA TURAI: Kotun Italy na neman gogarman gada-gadar Harkallar Malabu, Aliyu Abubakar

0

Alkalin wata babbar kotu a kasar Italy ya bada sammacen kamo tantirin dan kasuwar hada-hadar man fetur, Aliyu Abubakar, da a Abuja aka fi sani da A.A Oil.

Kotu ta nemi a gurfanar da shi ne saboda rawar da ya taka a harkallar dawurwura da sabarkalar cinikin Rijiyar Danyen Mai mai lamba ta OPL 255, harkallar da aka fi sani da Malabu Oil Scandal.

Kamfanin Dilancin Labarai na Reuters ya buga a ranar Laraba cewa masu gabatar da kara a Milan, babban birnin kasar Italy, su na zargin Aiyu da hannu wajen yin gada-gada a hada-hadar cinikin rijiyar danyen mai wadda aka rika buga-bugar sayarwa tare da shi.

Aliyu, hamshakin attajirin mai wanda ke da katafaren gidan alfarma na gani-na-fada, kuma sha kallo da ke kusa otall din Hilton a Abuja, an zarge shi da karbar dala milyan 550 daga cikin dala bilyan 1.1, wadanda kamfanin Shell da Eni suka biya a matsayin kudin cinikin Rijiar Mai mai lamaba OPL 245.

Ana tuhumar sa da shiga daka-dakar raba wadannan makudan kudaden da aka biya ta asusun kamfanin sa ga wasu manyan jigajigan gwamnatin Najeriya, a lokacin da aka sayar da rijiyar mai din.

An kuma yi zargin cewa an hada baki da jami’an gwamnati aka sayar da rijiyar danyen mai din a wulakantaccen farashin da aka ce darajar rijiyar ya nunka kudin da aka sayar da ita ba sau daya ba.

Sai dai kuma lauyan Aliyu Abubakar a Italy, mai suna Davide Pozzi, ya ce “Abubakar bai aikata wani laifi ba. Kuma ya kare kan sa a wurin da ya dace.”

ME AKE NUFI DA HARKALLAR ‘MALABU OIL’

A cikin shekarar 2011 ce aka yi wannan harkalla, inda wasu jami’an Najeriya suka yi dillanci, gada-gada da cuwa-cuwar sayar da rijiyar danyen man wadda ke Najeriya.

Kamfanin Shell da Eni ne suka sayi rijiyar akan kudi dala bilyan 1.1, kuma suka biya kudaden a asusun Najeriya.
Daga nan kuma aka karkatar da su a asusun Malabu, wani kamfani mallakar tsohon Ministan Harkokin Mai a Najeriya, Dan Etete.

Daga kamfanin Malabu ne aka karkatar da dala sama da 500 zuwa wasu asusun kamfanonin Aliyu Abubakar.

Bayan tashin-ballin ne aka fara bincike har kasashe shida, inda aka gano cewa a kokarin su na sayar da rijiyar a farashi mai rahusa, wasu jami’an gwamnatin Najeriya sun karbi cin hancin milyoyin daloli.

Har yanzu ana tabka shari’a a ltaly, inda ake tuhumar kamfanin Shell da Eni da kuma wasu mutane 13, cikin su har da Aliyu Abubakar.

YA AKA YI WASU SUKA RUFTA HARKALLAR MALABU?

Asalin harkallar dai Dan Etete ne a lokacin da ya na Ministan Harkokin Mai a Najeriya, ya sayar wa wani kamfanin da ya ke da hannu a ciki, mai suna Malabu Rijiyar Mai mai lamba OPL 245.

An zargi Shell da Eni da shiga harkallar bayar da zunzurun rabi kudin, wato dala milyan 520 domin rabawa ga Jonathan, wasu kusoshin gwamnatin sa da kuma wasu jami’an gwamnatin Najeriya.

An kuma zargi manyan shugabannin kamfanin Shell da na Eni da karbar dala milyan 50 kowanen su.

Yayin da ake ci gaba da binciken Aliyu Abubakar a kotun Italy, an rasa inda za a gan shi, balantana a aika masa da sammacin kamu.

Sai dai lauyan sa a Italy ya ce za a fara shari’ar sa gadan-gadan a ranar 14 Ga Mayu.

Amma tun daga watan Maris masu gabatar da kara za su fara gabatar wa kotu da tulin hujjojin su a kan Aliyu.

A nan Najeriya ana tuhumar Aliyu da Tsohon Ministan Shari’a Mohammed Adoke a Babbar Kotun Abuja da shiga harkallar Malabu.

An ce Aliyu ya kamfaci naira milyan 900 ya zuba a asusun Adoke a cikin watan Satumba, 2013.

An dai bayar da belin su bayan sun cika sharuddan beli.

Cikin watan Maris, Premium Times Hausa ta buga cikakken labarin irin rawar da Aliyu Abubakar da kuma Adoke suka taka a gada-gadar harkallar Malabu.

Waiwaye Adon Tafiya: Abin da ya faru a Kotun Italy Cikin 2019.

An ce Aliyu shi ne ya rika zama wani gogarman gada-gadar wasu manyan jami’an gwamnatin Goodluck Jonathan suka rika amfani da shi ya na karbar musu makudan milyoyin daloli.

Kotu na ci gaba da sheka masa ruwan tambayoyi dangane yadda aka karkatar da dala biliyan 1.1 daga kamfanin harkar main a Shell da Eni, harkallar da aka ce a tarihin hada-hadar mai ba a taba yin kamar ta ba a fadin Afrika.

Shell Da Eni: Manyan Kamfanonin Harkalla
‘Malabu Scandal’ Ita ce wata karimtsa-da-rimatson cuwa-cuwar zunzurutun kudade har dala bilyan 1.1 da kamfanonin hakar danyen main a Shell da Eni suka yi, tare da hannu da hadin bakin yin amfani da asusun ajiyar kudaden gwamnatin tarayyar Najeriya da dama.

An yi wannan karimtsa-da-rimatso ne a lokacin da Dan Etete ya na Ministan Harkokin Man Fetur na Najeriya. Kuma an tabbatar da cewa ba a taba yin harbat-ta-Matin harkalla kamar wannan ba a kamfanin Shell da Eni a fadin Afrika.

Daga cikin wasu asusun ajiya wanda Dan Etete ne kadai ke da hannu da ikon cirar ko da kwandala daga ciki ne aka rika rorar kudade ana zurarawa cikin asusun ajiyar kudi na dan gaga-gada Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da A.A Oil.

A.A Oil shi ne ke da wani katafarfen gida mai kallon otal din Hilton a Abuja. Gidan ya na kuma jikin farkon titin Gana Street da ke Maitama, Abuja. Ya na daya daga cikin kantama-kantaman gidajen alfarma a Abuja.

KARIMTSA-DA-RIMATSO

An ce an zurara har Dala milyan 520 cikin asusun sa.

Fadi-tashin binciken da aka rika yi ne aka gano cewa A.A Oil fa gada-gada ce ya ke yi wa wasu jami’an gwamnati, ba harkar gaban kan sa ba ce.

A cikin 2011 ne Goodluck Jonathan ya bada iznin ya cire kudaden a matsayin kudin biyan farashin Rijiyar Mai wadda ke da lamba OPL 245, daya daga cikin manyan rijiyoyin man da suka fi albarkar danyen mai kwance a karkashin su.

Da farko Shell da Eni sun nuna cewa su ba su ma san da wannan harkalla ba, ba su ci zomo ba, kuma ba a ba su ratayar ko da fatar zomo ba. Cewa suka yi ba su san kudaden a hannun Etete da ‘yan koren sa za su koma ba.

Sai dai kuma wasu hujjoji da PREMIUM TIMES ta mallaka, sun tabbatar cewa karya Shell da Eni ke yi, da su aka kaso zomo kuma da su aka gasa shi, sannan da su aka cinye naman sa.

A zaman yanzu da ana ci gaba da gurfanar da Shell, Eni, Etete, A.A Oil da wasu jami’ai da dama a wata kotun Italy da ke birnin Milan.

A ci gaba da shari’ar da aka gudanar a yau Laraba da safe, masu gabatar da kara sun sanar wa Mai Shari’a cewa wani lauyan kasar Italy wanda ya ce shi ne lauyan Abubakar Aliyu mai A.A Oil, ya kai musu ziyara jiya Talata inda ya tambayi a sake daga masa kafa domin a dan kara jinkirta shari’ar.

Amma kuma wani hamshakin lauya wanda ke aiki a Kamfanin Lauyoyin Barnaby Pace of UK Global Witness, wanda ya halarci zaman kotun ko a yau Laraba da safe, ya ce lauyan bai je kotu ba a yau, kuma bai aiko da dalilan rashin zuwan sa kotun ko da a rubuce ba.

KALLO YA KOMA KOTUN BIRNIN MILAN

Yayin da aka fara gabatar da bayanai a gaban mai shari’a, Aliyu ya tabbatar da cewa ya samu bayanan dukkan caje-cajen da ake yi masa.

Amma kuma ya ce shi zai iya kin amsa tuhume-tuhumen don kada gina wa kan sa rami kuma ya rufta da shi a gaban alkalin Italiya.

Sai dai kuma daga bayan PREMIUM TIMES ta samu tabbacin cewa lauyan da ke kare A.A Oil ya halarci kotun a birnin Milan a yau Laraba.

Haka kuma ita ma gwamnatin Najeriya akwai lauyan da ta tura da ke sauraren ba’asin bayanai kuma ya ke bibiyar shari’ar a cikin kotun.

Aliyu A.A Oil ya nemi a kara jinkirta masa lokaci, ta yadda sabbin lauyoyin sa za su yi nazarin yadda tuhume-tuhumen da ake yi masa suke, sannan kuma su san irin kamun ludayin da za su yi idan an fara sa-in-sa a gaban mai shari’a.

PREMIUM TIMES ta gano cewa masu gabatar da kara sai kwanan nan suka aika wa A.A Oil sammacin tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Cikin Maris, 2019, mai shari’a ya amince ya jinkirta wa Aliyu har zuwa lokacin da lauyoyin sa za su yi nazarin takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa. Ya ce caje-cajen da ake yi masa masu nauyi ne matuka, su na da bukatar lauyoyin sa su je su yi nazari.

Share.

game da Author