FARAWA DA BISIMILLAH: Yadda gwamna Bala ya dirka wa kamfaninsa kwangilar siyan motocin naira biliyan 3.9

0

Tun kafin ya zama gwamnan jihar Bauchi, EFCC suka rika tasa keyar sanata Bala Mohammed a bisa zargin watanda, cin hanci, karbar rashawa da wawushe kudin gwamnati a lokacin yana ministan Abuja.

Ba akai ga kotu ta yanke masa hukunci ba kan laifuffukan da EFCC ke tuhunarsa akai, kwatsam sai ya zama gwamnan jihar Bauchi inda ya kada gwamna mai ci a Mohammed Abubakar na APC a zaben 2019.

Daga darewar sa gwamnan jihar Bauchi sai gwamna Bala ya tsoma hannun sa cikin baitil malin jihar inda ya bai wa kamfanin da shima yana da hannun jari a ciki kwangilar siyan motoci har 105 don raba wa manyan ma’aikatan jihar da ‘yan majalisar jihar.

A wani binciken kwa-kwaf da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa har yanzu dai a bayanan dake kasa sannan ke a hukumar rajistan kamfanoni ta kasa CAC sunan gwamna Bala na jerin sunayen masu mallakin wannan kamfani.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ko a wadannan motocin da za a siyo sai da aka kara kudaden farashin su fiye da yadda aka saka tun a farko za a siya.

Bayan kauce wa ka’idojin da doka ta gindaya na yadda za abi da sai dole an tallata ire-iren manyan kwangiloli irin haka da tsohon kwamishinan kudin jihar Nura Soro ya ja kunnen gwamnati akai duk da kokarin saka wasu kamfanoni biyu a cikin bayanan takardun tallata gwangilar wai suma sun taya, gwamnati ta yi gaban kanta ne kawai ta amince wa wadda take so.

Haka dai daga baya a dalilin cakwakiyar da ta kanannade wannan kwangila kawai Soro ya hakura da kujerar kwamishinan da yake kai.

Sannan ko a cikin kasafin kudin jihar na 2019, naira biliyan 1 ne kacal aka amince a siyo motocin da su.

A binciken PREMIUM TIMES bayan haka sai kudin ya rikide daga naira biliyan daya zuwa naira biliyan 3.6, hakan ya nuna an kara naira biliyan 2.6 daga baya kenan.

Sai dai bamu iya sanin ko an koma majalisa domin gyara kasafin kudi da aka riga aka amince a dalilin wannan kari da aka yi.

Duka motocin da aka siyo wanda duk an kusa gama rabawa jami’an gwamnatin, an zuka musu kudi fiye da yadda farashinsu yake a kasuwa.

Kamfanin Adda

Bincike ya nuna cewa ita dai wannan kamfani an kafa ta ne tun a shekarar 1996 da hannun jari na naira 500,000, Sannan da masu hannun jari hudu.

Abdullahi Salihu Bawa ne ke da kaso mafi tsoka a jarin kamfanin na naira 200,000, sannan gwamna Bala da wasu mutane biyu na da hannun jarin naira 100,000 kowannen su.
 
Gwamna Bala yayi amfani da adireshin gida mai lamba 227, Titin Gombe a takardun yin rajistan wannan kamfani.

A binciken da PREMIUM TIMES ta yi game da wannan gida ta gano cewa wannan gida na mahaifin gwamna Bala, Sarki Duguri ne. Yanzu wasu ‘yan uwansa ke zama a gidan sai kuma idan wansa ya zo Bauchi Sallah, da yake shine yake rike da sarautar mahaifin su Sarki Duguri.

Bincike bai nuna mana ko waye Abdullahi Bawa ba a Bauchi domin kamfanin bata da shafi a yanar gizo da za a iya dubawa don sanin ko wacce irin kamfanine da wadanda suke da mallaki, da irin ayyukan ta zuwa yanzu.

Bugu da kari, bincike ya nuna cewa kamfanin ta sake nada gwamna Bala a matsayin darekta a wannan kamfani a 2006 a hukumar CAC

Amma kuma dukka takardun da aka faffalle, aka dudduba, aka bincika, aka bi layi-layi daki-daki ba a ga inda gwamna Bala yayi sallama da wannan kamfani ba.

Sai dai ma ganowa da aka yi a takardun bayanai na kamfanin daga 2006 – 2018 cewa gwamna Bala yana nan daram a matsayin darekta a wannan kamfani, har a lokacin da yake ministan Abuja, da haka ma karya doka ce.

A haka ne kuma, a daidai lokacin da za a ba wannan kamfani kwangilar, sai kamfanin ta sanar wa CAC a watan Agustan 2019 nadin wani amini kuma makusancin Bala, mai suan Abdullahi Yari a matsayin Sakataren Kamfanin.

PREMIUM TIMES, ta nemi ji daga bakin kakakin gwamnatin jihar Bauchi Mukhtar Gidado, inda ya tabbatar da lallai gwamnatin jihar ta ba da kwangilar siyo wadannan motoci har guda 105, sannan ya tabbatar da cewa lallai kusan duka sun shigo kasa Najeriya har ma an raba su, sauran da suka rage suna sa ran za su iso jihar Bauchi nan da kwanaki kadan masu zuwa.

Sai dai kuma ya gargadi PREMIUM TIMES da ta je ma’aikatar yi wa kamfanoni rajista CAC domin tantance ainihin sahihancin wannan kamfani da ta ce har yanzu gwamna Bala na da hannun jari a ciki domin a nan ta yi kuskure ba haka bane.

Daga baya da aka aika masa da hujjojin da kuma takardun tabbacin haka da sai ya kauce, ya tsuke bakin sa yayi shiru har yanzu bai ce komai akai ba.

READ: EXCLUSIVE: Bauchi Gov. Bala Mohammed awards N3.6 billion contract to own company

Share.

game da Author