Tsohon gwamnan jihar Barno Sanata Kashim Shettima ya yi kurin cewa duk da ihun da aka yi wa Buhari a Barno, mutanen jihar na son sa matuka.
Idan ba a manta ba mutanen jihar Barno sun rika yi wa Buhari Ihu suna cewa ” Bamu su, Bamu so” a ziyarar da ya kai ranar Laraba garin Maiduguri bayan kisan kiyashi da Boko Haram suka yi wa wasu matafiya a garin Auno.
Wannan abu da ya faru bai yi wa fadar gwamnatin Buhari dadi ba domin shi kansa Buhari yana tinkaho da soyayyar da yake samu daga mutanen jihar Barno.
” Mutane sun saka burin su ga Buhari, sannan kuma basu san cewa shi Buhari mutum ne ba wani boka ko mai sihiri ko mai siddabaru ba da zai iya canja komai ko kuma yayi yadda yake so a lokacin da yake so.
” Tabbas mutane sun kai makura, tashin hankali ya kai intaha, amma kuma abinda zan fadi a nan shine komai zai zo karshe wata rana. Har yanzu mutanen yankin Arewa Maso Gabas da jihar Barno na matukar kaunan Buhari.
” Sannan kuma ku duba ku gani. Buhari ne ya nada yan asalin jihar Barno manya mukamai musamman wanda ya shafi tsaro. Buhari ya nada Tukur Buratai, babban hafsan sojojin Najeriya, sannan ya nada Monguno mai bashi shawara kan harkokin tsaron kasa.
Da aka tambaye shi ko me zai ce game da zargin shugabannin jihar da Buhari yayi cewa sune suka kasa maida hanakali wajen ganin an kawo karshen wannan matsala, shettima ya ce bai tabbatar cewa Buhari zai furta wannan kalamai ba.
A nawa fahimtar Buhari na nufin mutane ne baki daya da a hadu a tunkari matsalar kai tsaye. Amma ba wai yana dorawa wani laifi bane.