Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara amfani da dokokin hana siyar da taba sigari a kasar nan.
Wadannan kungiyoyi wanda a ciki akwai ‘Nigeria Tobacco Control Alliance (NTCA)’ da ‘Environmental Rights Action/Friends of the Earth Nigeria (ERA/FoEN)’ sun yi wannan kira ne ranar Laraba a Abuja.
Kungiyoyin sun ce rashin fara aiki da wadannan dokoki na iya kawo cikas ga kiwon lafiyar mutane a dalilin illolin dake tattare da busa taba Sigari.
Da yake tofa albarkacin bakinsa akai mataimakin shugaban kungiyar ERA/FoEN Akinbode Oluwafemi ya ce kungiyoyin suna bibiyan kokarin canja fasalin aiyukka da kamfanonin sarrafa taba sigari ke yi tun da aka yi wadannan dokoki.
Oluwafemi ya ce rashin fara amfani da wadannan dokoki zai bai wa wadannan kamfanoni damar ci gaba da cutar da kiwon lafiyar mutane musamman matasa.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta bude asusu da zai taimaka wajen ganin kamfanonin sarrafa taba, masu safaran taba da masu shan taban su rika kiyayewa da bin doka.
Daga nan jami’ar kungiyar ‘Campaign for Tobacco-Free Kids’ Hilda Ochefu ta yi kira ga duk sassan gwamnati, hukumomi da masu ruwa da tsaki da su hada hannu wajen ganin an fara amfani da wadannan dokoki a Najeriya
Idan ba a manta ba a 2015 gwamnatin Najeriya ta kafa dokar hana siyar da taba sigari musamman ga matasa ‘yan kasa da shekara 18.
Dokar ta kuma hana matasa irin haka yin tallar sigarin da tallata ta a gidajen talabijin da radiyo na kasar.
Gwamnati ta yi haka ne saboda sakamakon biniciken da ya nuna cewa kashi 15.4 bisa 100 na mutanen Najeriya (Maza da mata) na busa taba sigari sannan kashi 89 bisa 100 na matasa ‘yan shekara 18 ne suka fi siyan ta, wato amfani da ita.
Sakamakon binciken ya nuna cewa babban birnin tarayya Abuja ta fi yin kaurin suna wajen yawan masu busa taba sannan jihohin Ekiti, Katsina da Edo.