Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya fallasa cewa akwai wasu manyan gardawan da ke hana ruwa gudu wajen kamo Diezani Allison-Maduekwe, domin a maido ta Najeriya a hukunta ta.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai a Kaduna, Magu ya ce, tsohuwar Ministar Harkokin Man Fetur a lokacin mulkin Goodluck Jonathan din ta saci akalla dala bilyan 2 da rabi.
Kowace dala bilyan daya dai ta na daidai da naira bilyan 360 a farashin gwamnati.
Idan ba a manta ba cikin watan Janairu, Magu ya taba cewa akwai sa hannun wasu kasashe wajen kokarin dakile dawo da Diezani domin a hukunta ta.
“Can baya na je London, kuma ni da jami’an su mun rika gudanar da bincike a wurare. Ina shaida musu cewa Najeriya na bukatar makudan kudaden da aka sato aka boye a kasashen ketare, domin ta yi amfani da su bunkasa tattalin arzikin ta.
“Amma abin mamaki, duk da irin hannun da Diezani ke da shi dumu-dumu wajen satar makudan kudaden kasar nan, akwai wasu manyan gardawa masu hana ruwa gudu da basu so a maido ta domin a kara bincikar ta da kuma hukunta ta.”
Diezani dai na zaune a London, tun bayan ficewar da ta yi bayan faduwa zaben da gwamntin Jonathan ta yi a 2015.
A nan Najeriya an ci gaba da binciken ta da kuma kwace manyan kadarorin da ta mallaka, to amma har yanzu ba a kai kan makudan kudaden da ake zargin ta boye a kasashen waje, musamman Ingila ba.
A wurin taron, Magu y ace EFCC ta gurfarnar da mutum 103 cikin 2015, mutum 195 cikin 2016, wasu 314 a cikin 2018 sai kuma mutum 1215 a cikin 2019.
‘Magu Ya Cika Surutu’ –Wani dan taratsi
Wani lauya kuma dan taratsin kare hakkin jama’a da ke zaune a Lagos mai suna Inibiche Effiong, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Magu ya cika suturai kamar an bude kan famfo.
“Kamata ya yi ya fito ya shaida wa duniya sunayen mutane ko manyan gardawan da ya ke ta cewa su na kawo cikas wajen sake maido Diezani domin a hukunta ta.
“Ni dai na san akwai ma lokacin da ita din da kan ta ta ce za ta kawo kan ta domin ta kare kan ta a kotu, amma su EFCC din ne ma suka ki amincewa. To wane bobbotai kuma zai rika fitowa ya na yi mana a yanzu.
“Idan ma Diezani na wata kasa, ai akwai dokar yarjejeniya tsakanin Najeriya da Birtaniya, wadda suka amince a yi musayar masu laifi ko kuma a damka wa juna masu laifi. Me ya sa Magu ko Najeriya ba za ta bi wannan tsarin ba, sai shi Magu ya rika surutai a jaridu kawai?”
Daga nan ya roki Magu da ya ja bakin sa ya yi shiru, domin idan ana so a maido Diezani, su Magu din sun fi kowa sanin hanya mafi sauki, ba sai ya shiga jaridu ya na kartar kasa ba.
Magu dai ya ce ba don Diezani na da ‘yancin zama a karkashin sa-idon Birtaniya ba, da za su iya damko ta domin a hukunta ta a nan Najeriya.